1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalilin yin sauyin lokaci a nahiyar Turai

Sadissou YahouzaApril 23, 2013

A kan yi sauyin lokaci sau biyu a nahiyar Turai a dukannin shekara wato a karshen watan Maris da kuma karshen watan Oktoba.

https://p.dw.com/p/18LRL
Hoto: Fotolia/Dan Race

A dukannin ranar Talatin da daya ga watan Maris na kowacce shekara a kan yi karin awa guda a agogunan kasashen nahiyar Turai, lamarin da ya kan sa ake samun banbancin lokaci tsakanin kasashen na nahiyar Turai da kuma takwarorinsu na nahiyar Afrika irin su Tarayyar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Masana ilimin muhallin dan adam wato Geography, irin su Farfesa Adamu I. Tanko na Jami'ar Bayero da ke Kano a Najeriya sun shaida cewar sauyin lokacin na da nasaba da yawaitar tsayin rana da ake samu bisa yadda dare ya ke a nahiyar ta Turai musamman ma dai a irin wannan lokaci na bazara. Ana yin sauyin ne duba da yadda abubuwa za su daidaita domin komai ya tafi yadda ya ake so.

Baya ga wannan dalili, mahukunta sun dau aniyar yin wannan sauyi na lokaci ne cikin farko shekarun 1970 lokacin da aka samu matsala ta makamashi inda ake rage awa guda kan lokaci ko karin awa guda wanda kan taimaka wajen daidaituwar abubuwa da kuma yin tsumin makamashi.

Shi dai wannan sauyin lokaci wanda har wa yau ake yin sa lokacin sanyin na da tasiri wajen bacci domin a kan samu karancin bacci lokaci bazara, yayin da a lokacin sanyi kuma ake samu isasshen lokacin bacci da kuma karanci rana domin rana kan fadi ne 'yan mintuna kalilan bayan karfe hudu na yamma.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Sadisou Madobi