1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwa a kan rashin tsaro a Najeriya

Zainab MohammedJune 30, 2014

Sake fuskantar ƙarshen mako ana kashe-kashen jama’a da kai hare-hare a wasu sassan arewacin Najeriya ya sake jefa jama'a cikin wani hali na rashin tabbas.

https://p.dw.com/p/1CSoY
Nigeria Anschlag in Abuja 25.06.2014
Hoto: picture-alliance/AP Photo

To ƙarshen makon dai ya kasance cike da tashin hankali ga al'ummar Najeriyar waɗanda suka fuskanci ƙaruwar kai hare-hare kama daga jihar Bauchi zuwa jihar Borno inda fiye da mutane 51 suka mutu. Ya zuwa jihohin Kadauna da Taraba dukka labarin ɗaya ne dai na kissan jama'a da raba wasu da muhallansu a yanayin da ke nuna ƙara taɓarɓarewar matsalar rashin tsaro a Najeriyar.

Fargarbar yin amfani da siyasa domin tada fitina gabannin zaɓen shekara ta 2015

Ko da yake gwamnatin Najeriyar na mai danganta hare-haren ga masu gwagwarmayar kai wa ga madafan iko saboda tinkarar zaben 2015, amma wakilai masu lura da al'amuran da ke faruwa musamman a Kaduna da Taraba na da wasu dalilai na daban. Wannan ya sanya Air Commodore Ɗan Suleiman bayyana cewar dole ne fa a yi taka tsan-tsan a cire cusa siyasa a lamarin.

Nigeria Anschlag in Abuja 25.06.2014
Hoto: picture-alliance/AP Photo

‘' Yakamata a cire siyasa a cikin wannan batu na rashin tsaro domin ba batun siyasa ba ne, domin idan ka duba ƙasashen Turai da muke koyi da su idan irin wannan abu ya taso, ba a sa siyasa. A ce ana kashe-kashe ana ɓarna abu ne da ke tada hankalinmu, mun yi yaƙi ne don mu samu zaman lafiya a Najeriya amma yanzu babu wannan yana bata mana rai''.

Ci gaba da zubar da jinin bani adama a sassan arewacin Najeriyar na zama abin da ke ɗaga hankalin al'umma da sannu a hanakli, saboda yadda ake samu asarar ta rayukan jama'a mai yawan gaske.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da wasu rahotannin da wakilanmu na Jos da Kaduna suka aiko mana dangane da lamarin na tsaro da ma tattuanawa tsakanin addinai a Najeriyar.

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane