1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwa kan tawaye a Afirka ta tsakiya

March 16, 2013

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fargaba game da halin da fararen hula za su shiga a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya bayan sake barkewar tawaye a yankin Kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/17yq8
Hoto: SIA KAMBOU/AFP/Getty Images

Hukumar 'yan gudu hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa sake daukan makamai da 'yan tawayen jamhuriyar Afirka ta tsakiya suka yi na barazana ga rayukan fararen hula a yankin kudu maso gabashin kasar. Bayanan da suke zuwa mana daga Bangui babban birni sun nunar da cewa gamayyar Kungiyoyin tawaye ta Seleka ta yi fito na fito da dakarun gwamnati a cikin wannan makon tare da mayar da biranen Banguassou da gambo karkashin kulawarsu.

Ita dai Seleka ta zargi gwamnati da rashin mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma a baya wadda ya tanadi sako dimbin fursononin siyasa da ke tsare. Gwamnatin Francois Bozize ta yi tir da wannan mataki tare da danganta shi da mayar da hannun agogo baya. Watannin biyun da suka gabata ne dai bangarorin biyu suka tsagaita bude wuta tare da kafa gwamnatin hadaka da nufin kawo karshen sabanin da ke tsakaninsu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas