1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Dandalin Matasa: Makon Social Media a Legas

Abdul-raheem Hassan MNA
February 27, 2020

Saboda tasirin shafukan sada zumunta ne musamman tsakanin matasa, shirin ya karkata akalarsa kan makon shafukan sadarwar da aka bude a birnin Legas da ke kudancin Najeriya. 

https://p.dw.com/p/3YWX5

Sama da mutane biliya hudu ke mu'amala da yanar gizo a duniya, kuma Indiya ce ke kan gaba da kusan mutane miliyan 54.

Kuma a shafukan sada zumunta Facebook ya yi zarra musamman a nahiyar Afirka, da kusan mutane miliyan 120 ke amfani da shi, kuma na kimanin kashi 80 cikin 100 an fi yin Facebook din ta waya.