1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantaka takanin Jamus da Turkiyya na kara yin tsami

Mohammad Nasiru Awal AS
July 20, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus ta ce tsaurara matakai kan Turkiyya ya zama dole da ba za a iya kauce masa ba.

https://p.dw.com/p/2gtTL
Deutschland Bundeskabinett Gabriel und Merkel
Sigmar Gabriel da Angela Merkel bayan wani taron majalisar ministocin Jamus a BerlinHoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana furucin da ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya yi na sauya alkiblar manufar siyasar Jamus dangane da kasar Turkiyya da cewa abu ne muhimmi da ya zama wajibi a dauka.  Da farko dai a martanin da ya mayar dangane da kame wani Bajamushe mai faftukar kare hakkin dan Adam wato Peter Steudtner da wasu mutane da Turkiyya ta yi, ministan harkokin waje Gabriel ya ce za a tsaurara bayanai kan tafiye tafiye zuwa Turkiyya, yana mai cewa ana gallaza wa Jamusawa da ke zuwa Turkiyya, abin da ke jefa su cikin rashin tabbas.

Ya ce: "Har yanzu akwai kyakkyawar hulda tsakanimu da Turkiyya. Muna son kasar ta zama daya daga cikin kasashen yamma. Amma take-taken gwamnatin Turkiyya a yanzu ya sa a dole Jamus za ta yi nazari kan dangantakarta da Turkiyya. Matakin farko da muka dauka shi ne ba da sabbin shawarwari ga Jamusawa da ke kai ziyara Turkiyya."