1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar KTT da Kasashen Tsakiyar Afurka

September 9, 2004

A yau alhamis ne wakilin Kungiyar Tarayyar Turai akan al'amuran kasashen tsakiyar Afurka Aldo Ajello ya gabatar da bayani a game da sakamakon ziyararsa da ya kai zuwa yankin baya-bayan nan

https://p.dw.com/p/Bvga

An yi shekara da shekaru ana fama da zaman dardar a yankin kuryar tsakiyar nahiyar Afurka. Misali a kasar Kongo, sai a shekarar da ta wuce ne kasashe bakwai dake da hannu a yakin basasarta suka janye dakarunsu daga harabarta. A Burundi kuwa mutane sama da dubu 300 suka yi asarar rayukansu sakamakon rikicinta da ya ki ci ya ki cinyewa, a yayinda makobciyarta Ruwanda ta fuskanci kisan kare dangi akan ‘yan kabilar tutsi a shekarar 1994. A baya-bayan nan an fuskanci barazanar sake billar sabbin tashe-tashen hankula sakamakon kisan gillar da aka yi wa ‘yan Tutsi su 160 a sansaninsu na gudun hijira a Burundi watan augustan da ya wuce. A lokaci guda kuma an shiga tababa a game da makomar hada-hadar neman zaman lafiyar Kongo saboda kurarin janyewar da wata kungiyar tawaye tayi daga gwamnatin hadin gambiza ta kasar. Shi dai kisan gillar da aka yi wa ‘yan gundun hijirar a Gatumba dake Burundi na daya daga cikin mummunar tabargazar da aka shaidar a wannan yanki tun bayan ta’asar kisan kiyashin na Ruwanda shekaru goma da suka wuce. A wannan karon ma daidai da wancan, ‘yan Hutu ne suka kai hari tare da halaka ‘yan Tutsi. Domin kuwa akalla kungiyar tawaye ta ‘yan Hutu mai kiran kanta wai kungiyar neman ‘yancin kan Burundi ta ce ita ce ke da alhakin wannan danyyen aiki. Wakilin kungiyar tarayyar Turai akan al’amuran yankin tsakiyar nahiyar Afurka Aldo Ajello ya kai ziyara Gatumba domin gane wa idanunsa abin da ya faru, inda yake cewar:

O-Ton..

Abin dai ba kyan gani, ta’asa ce ta kisan kare dangi akan ‘yan Tutsi. Masu alhakin harin ba su tausaya wa mata ko yara kanana da jarirai ba. Wajibi ne MDD ta bi bahasin lamarin. A kuma fito fili a fadi sunayen masu alhakin wannan danyyen aiki a kuma hukunta su nan take.

Wadanda suka tsallake rijiya da baya sun yi nuni da cewar masu laifin kai harin sun hada da ‘yan hutun Ruwanda da kuma dakarun sojan kasar Kongo. Wannan kisan kiyashin ka iya zama sanadin billar wani sabon rikici a wannan yanki kamar yadda aka ji daga bakin Aldo Ajello. Dangane da kasar Kongo kuwa, inda kungiyar tawaye ta RCD-Goma tayi barazanar kakkabe hannuwanta daga gwamnatin hadin gambiza da aka nada a fadar mulki ta Kinshasa Ajello ya ce an samu kafar shawo kan takaddamar tun kafin lamarin yayi tsamari saboda kungiyar tuni ta amince ta sake dawowa ana damawa da ita a gwamnatin ta hadin gambiza. Ana kuma tattaunawa domin shawo kan matsalolin da suka sanya ta nemi janyewa daga Kinshasa. To sai dai kuma duk da wannan ci gaba har yau da sauran rina a kaba kafinal’amura su daidaita a kasar kongo. Domin kuwa dukkan masu hannu a rikicin kasar, gwagwarmaya suke wajen dora hannu akan dimbim albarkatun da Allah Ya fuwace mata.