1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dattawa sun yi tir da wa'adi ga kabilar Igbo

June 7, 2017

Dattawan arewacin Najeriya da sarakunan Yarbawa da na Igbo sun bayyana rashin goyon bayansu ga kiraye-kirayen kungiyoyin matasan arewacin kasar kan bukatar ‘yan kabilar Igbo su tattare cikin watanni uku.

https://p.dw.com/p/2eG8P
Protestierende Studenten während ASUU Streik in Kano
Hoto: DW/N. S. Zango

A karon farko wasu dattawa daga jihohin arewacin Najeriya da malaman jami'o'i tare da daukacin masu rike da mukaman gargajiya na kabilun kudancin kasar da ke zaune a yankin jihohin Najeriya sun fito ta kafafen watsa labarai inda suka nuna rashin amincewarsu ga kiraye-kirayen kungiyoyin matasan arewacin na bukatar kabilar da su kauracewa arewa, lamarin da masana tarihi da zamantakewa daga jami'o‘in kasar ke ganin zai haddasa rigima a cikin kasar.

Dr. Mohammad Ibrahim da ke koyarwa a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria bayyanawa ya yi da cewa babu abin da zai taba raba alu‘mar wannan kasa, saboda haka suke ganin cewa duk yunkuri ne na kawo koma baya ga hadin kan wannan kasar ba za ta taba samun nasarar da ta ke bukata ba.

Dr. Mohammed ya ce: 

‘‘Tun kimanin shekaru 100 ne muka kasance muna tare, a saboda haka babu wani abin da zai taba hada Inyamurai da Yarbawa da Hausawa fadawa cikin wani sabon tashin hankali. Muna ganin bai dace ba wasu gungun matasa su haddasa matsaloli a cikin kasar domin suna san kafa wata kasar"

Die Last auf den Schultern der neuen Regierung - Nigeria vor der Wahl Flash-Galerie
Hoto: DW/Stefanie Duckstein

A kan wannan batu dai yanzu haka kungiyar tuntuba ta dattawan jihohin arewacin Najeriya na wani taron gaggawa, haka zalika rahotanni na nuni da cewa jami'an tsaro ma suna na gudanar da tarurruka.

Dattawan arewa da suke nuna rashin goyan bayansu ga kiraye-kirayen matasan na su kamar dai yadda Dattijo Usman Lapai da Baba Danlami Adamu ke cewa

‘‘Babu wani tsohon da ya san abin da faru lokacin yakin basasa a wancan zamani da zai sake bayar da wata dama kitsa wani rikicin ba, a saboda haka muna janyo  hankalin dattawa da sarakunan yankin dukkanin bangarorin Najeriya a kan wayar da kan matasansu muhinmancin zaman lafiya‘‘

Ra'ayin Yarbawa

Alhaji Muhammadu Arribabowa shi ne dai shugaban sarakunan yarbawan arewa, kuma jakadan zaman lafiya a Najeriya da shi ma ke ganin cewa akwai bukatar gudanar da wani taron gaggawa na dukkanin sarakunan gargajiya da gwamnati tare da malaman addinai a kan hanyoyin magance ire-iren wadannan matsaloli.

Ya ce ‘‘babu wanda zai iya raba wannnan kasar, domin Allah da ya hada mu tare yana son ganinmu tare, kuma duk wani da ke wani yunkurin sake tayar da hankalin aluma. Allah baya tare da shi, a saboda haka muna yin kira ga gwamnatin tarayyar kasar a kan tashi tsaye wajen gudanar da wani taron gaggawa na kasa a kan bullo da hanyoyin tattaunawa kan magance ire-iren wadannan matsalolin da ke maida hannun agogo baya‘‘

Martanin kabilar Igbo 

Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Hoto: Getty Images/AFP

Barista Christ Nnole shi ne dai mukaddashin shugaban kabilar Igbo mazauna jihohinn arewacin Najeriya 19 da ke kira ga zaman lafiya tsakanin dukkanin kabilun.

Ya ce ‘‘muna kira ga daukacin al‘umar mu da ke zaune a jihohin arewacin kasar a kan zaman lafiya, za mu ci gaba da yin kira ga dorewar zaman lafiya a cikin wannan kasar. Abin da ya kamata a lura da shi, shi ne na wajen tabbatar da ganin cewa gwamnati a dukkanin matakai tana gudanar da adalcin da ya kamata a rika gudanarwa domin samun ci gaban kasa da al‘uma baki daya‘‘

Bukatun kungiyoyin matasan arewan da suka bai wa kabilar Igbo wa'adin watanni uku su bar yankin dai su ne, na magance yadda ‘yan gwagwarmayar kafa kasar Biafra ke haddasa rudani da ke neman ballewa da kuma daina kai hare-hare kann Hausawa mazauna kudu masu gabashin kasar tare da kallon da ake yiwa arewa a matsayin masu dogaro da tattalin arzikin yankin Naija Delta.