1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'in MDD de Mistura ya nuna shakku kan Amirka

February 19, 2017

Yayin da aka kammala taron koli kan tsaro a birnin Munich jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya baiyana shakku kan kudirin Amirka na kawo karshen yakin Siriya.

https://p.dw.com/p/2XsXE
Deutschland Münchner Sicherheitskonferenz 2017
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Balk

A karshen taron koli kan al'amuran tsaro a duniya da aka kammala a birnin Munich na Jamus, babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Staffan de Mistura ya baiyana shakku akan kudirin shugaban Amirka Donald Trump wajen kawo karshen yakin Siriya 

Kalaman na De Mistura na zuwa ne yan kwanaki gabanin sabon zagayen tattaunawar sulhu da za'a gudanar a Geneva. Jakadan na Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa taron na Munich a akan tsaro cewa rashin sanin inda Amirka ta sa gaba ya sanya gano bakin zaren warware rikicin da ya kai ga yakin basasar da aka kwashe shekaru shida ana fafatawa a Siriya yin matukar wahalar gaske. 

Deutschland Unklarheit über Trumps Außenpolitik prägt Sicherheitskonferenz in München | de Mistura
Hoto: Reuters/M. Rehle

Yace Ina Amirkar ta ke a duk tsawon wannan lokaci? yace ba zan iya gaya muku domin ban sani ba, amma abin da zan iya fada shine na fahimci suna da abin da suka kudire wanda suka fi baiwa muhimmanci. Wadannan kuwa sune yakar Daesh da rage tasirin wasu manyan kasashe masu karfin tasiri a yankin da kuma yin kafa kafa kada ta sabawa daya daga cikin manyan kawayenta a yankin.

A jawabinta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga Amirka da sauran kasashe su bada cikakken hadin kai ga kawancen kungiyar tsaro ta NATO tare da kasancewa tsintiya madauriki daya domin tukarar kalubalen na tsaro. 

Deutschland Münchner Sicherheitskonferenz 2017
Hoto: Reuters/M. Rehle

Ta ce na yi imani kalubalen da muke fuskanta yanzu a duniya, babu kasa daya da za ta iya tunkararsa ita kadai ana bukatar hada karfi wuri guda. Wannan ya sa na ke jaddada cewa wajibi ne a sami hadin kan gamaiyar kasa da kasa domin yin tasiri da gagarumar nasara.

Sai dai kuma ba tare da bata lokaci ba mataimakin shugaban Amirkan Mike Pence ya nemi kwantar da hankali game damuwar da ake da ita musamman game da kalaman Donald Trump da ya baiyana kawancen kungiyar tsaron NATO a matsayin tsohon yayi. Yace Amirka na goyon bayan kungiyar kawancen tsaro ta NATO kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba a wannan kawance tsakanin Nahiyar da Amirka. 

Deutschland Münchner Sicherheitskonferenz 2017
Hoto: Reuters/M. Rehle

Yace gwagwarmayar ku gwagwarmayar mu ce samun nasarar ku samun nasarar mu ce, wannan shine alkawarin shugaba Trump. Za mu tsaya kafada da kafada da nahiyar Turai a yau da kuma a ko da yaushe saboda mun hade akan kyawawan akidu da suka hada da yanci da dimokradiyya, adalci da kuma tafarkin shari'a.

Sauran batutuwan da taron ya yi nazari akan su sun hada da duba hanyoyin sake gina kasashen Libya da Siriya da yaki ya yiwa kaca kaca da kuma hanyoyin aiwatar da kudirorin cigaba mai dorewa.

Shi dai taron kolin kan al'amuran tsaro da aka yiwa lakabi da "Munich Conference" an kafa shi ne a shekarar 1963 da manufar hada kan shugabanni siyasa dana tattalin arziki daga sassa daban daban na duniya ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar a tsakanin kasashe.