1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban jama'a sun gudanar da zanga zanga a Rasha

November 4, 2012

Tun bayan sake kama ragamar uilki a Rasha, shugaba Putin na fuskantar mummunar adawa inda ake yawaita zanga zangar kyamar gwamnatinsa.

https://p.dw.com/p/16cjV
Hoto: DW/A.Sawitzky

Rahotanni daga Mosko babban birnin ƙasar Rasha, sun tabbatar da fitowar dubun dubatan mutane a kan tituna a wannan Lahadin domin nuna ƙyama ga mulkin shugaban ƙasar Vladimir Putin wanda ya haye karagar ikon ƙasar a shekarar bara. A cewar hukumomi kimanin mutane dubu 30 ne ke zanga zangar yayin da waɗanda suka tsara boran ke cewa aƙalla adadin jama'an da suka fito a duk faɗin ƙasar ya lunkan da kusan kashi huɗu.
Wannan zanga zangar ta zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke shugulgulan zagayowar ranar haɗin kan 'yan ƙasa bayan mulkin mallakar da ƙasashen Polsand da Lithuaniya suka wa ƙasar ta Rasha shekaru 400 da suka gabata. Tuni kuma hukumomin 'yan sanda suka bayyana cewar yanzu haka dai an cafke kusan mutane 90 daga cikin masu zazzafen ra'ayin zanga zangar da gwamnatin ta haramta tun can farko.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Mohammad Nasiru Awal