1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na bukatar sabbin matakan yaki da sauyin yanayi

September 23, 2014

Masu fafutukar kare muhalli na kallon wannan taro a matsayin wani dandali mai muhimmanci da zai tattaro masu adawa da gurbatar ta muhalli a duniya.

https://p.dw.com/p/1DJ6E
Proteste in Indien vor dem UN-Klimagipfel am 23.09.2014
Hoto: AFP/Getty Images

A yau Talata ne aka bude babban taron shugabanni na duniya kan sauyin yanayi da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara, inda aka bukaci aiwatar da tsare-tsare da aka samar kan matakan yaki da ci gaban dumamar yanayi.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, shi ya karbi bakuncin shugabannin daga kasashe 120, da ke zama wani babban taro tun bayan taron Copenhagen a shekarar 2009 shi ma kan sauyin yanayin da ya gaza cimma wani abun azo a gani cike da rudani.

Jami'an diflomasiya da masu fafutukar kare muhalli na kallon wannan taro a matsayin wani dandali mai muhimmanci da zai tattaro masu adawa da gurbatar ta muhalli kafin taron da za a yi a birnin Paris a karshen shekarar 2015 wanda zai kai ga kulla wata yarjejeniya da za ta kawo hanyoyin da za a bi wajen rage sinadaran iskar gas da ke gurbata muhalli da aka fi sani da greenhouse gases bayan shekarar 2020.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu