1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya ta shirya don ceto Mali daga masu kishin addini

October 19, 2012

Bayan da Kwamitin Sulhu ya amince da tura sojoji a ƙasar dake yammacin Afirka, ita ma EU ta ce za ta taimaka bisa manufar fatattakan 'yan Islama daga arewacin Mali.

https://p.dw.com/p/16TGA
Hoto: AP

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan rikicin ƙasar Mali. A labarinta mai taken Mali matattarar rikici, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa gamaiyar ƙasa da ƙasa ce kaɗai za ta iya daidaita al'amura a ƙasar dake yankin yammacin Afirka, sannan sai ta ci-gaba kamar haka.

“Halin da ake ciki a arewacin Mali ya na da babban hatsari, da ba za a iya magancewa ba sai da taimakon ƙasashen duniya. Ƙungiyar Al Qaida da wasu ƙungiyoyi masu ƙwarƙwaryar alaƙa da Al Qaida sun addabi arewacin ƙasar dake yankin Sahel. Rundunar sojan Mali ta zama tamkar wani kare da ba ya haushi balantana cizo. Saboda haka abin yabawa ne shawarar da Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya yanke, inda ya amince da tura sojoji domin ceto yankin na arewacin Mali daga hannun masu kaifin kishin Islama. Sai dai wani ciƙas da wannan mataki zai iya fuskanta shi ne manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arziki ba za su ba da karo karon sojojinsu ba, in ban da taimakon kayan aiki da na fasaha, wato kenan ƙasashen Afirka ne kaɗai za su tura sojojin da za su fatattaki 'yan tawayen daga arewacin ƙasar ta Mali.“

EU za ta shiga cikin aikin ceto Mali

Ƙungiyar tarayyar Turai EU za ta shiga ƙasar Mali inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai rawaito majiyoyin diplomasiya na cewa masu ba wa sojoji shawara za su marawa sojojin Mali da ba su da cikakken horo don su yaƙi 'yan aware na Islama.

Dirk Niebel in Mali
Ministan raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel lokacin ziyararsa a MaliHoto: picture-alliance/dpa

„Ƙungiyar EU na shirye shiryen tafiyar da wani aikin soji a Mali wadda ta dare gida biyu tun bayan boren masu kishin Islama dake samun goyon bayan ƙungiyoyin ‚yan ta'adda. Bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da tura sojojin ƙasashen duniya a Mali domin sake mayar da ƙasar tsintsiya maɗaurinki ɗaya, a farkon wannan mako ministocin harkokin wajen ƙasashen EU suka gabatar da shirin tura sojoji ƙarƙashin manufofin tsaro na nahiyar Turai. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin wata tattaunawa a birnin Bamako a wannan Juma'a tsakanin Majalisar Dinkin Duniya, ƙungiyar ECOWAS da ƙungiyar tarayyar Afirka da kuma gwamnatin Mali game da matakan da za a ɗauka."

Katse hanzarin magoya bayan Gbagbo

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung labari ta buga game da cafke wasu masu biyayya ga tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo a Ghana. Ta ce:

„Mahukunta a ƙasar Ghana sun kama mutane 43 ‚yan ƙasar Cote d'Ivoire magoya bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo ne. Ana zargin su da shirya wata makarƙashiyar sake karɓe mulkin ƙasarsu da ƙarfin soji. An cafke su ne yayin wani samame da aka kai a kan wani sansanin ‘yan gudun hijira dake kusa da garin Takoradi mai tashar jiragen ruwa dake kudu maso yammacin ƙasar Ghana. Hakan dai yazo ne bayan wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya da ya shiga hannun kafofin yaɗa labaru a makon da ya gabata, wanda a ciki aka nuna cewa magoya bayan Laurent Gbagbo da suka yi ƙaura a Ghana sun kafa wani sansanin mayaƙa da nufin dagula al'amura a Cote d'Ivoire. A watannin baya bayan nan dai ‘yan bindiga da ake zargi ‘yan Cote d'Ivoire ne a Ghana sun yi ta kai hare hare a yankin kan iyakar ƙasar da Ghana.“

Elfenbeinküste Laurent Gbagbo
Ana zargin magoya bayan Laurent Gbagbo da shirin ta da zaune tsayeHoto: picture-alliance/dpa

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu