1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola tana barazana wa tattalin arziki

August 14, 2014

Cutar Ebola ta fara karar tsaye wa harkokin tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma

https://p.dw.com/p/1Cv1R
Hoto: picture alliance/AP Photo

Cutar Ebola tana barazanar tattalin arziki wa kasashen yankin yammacin Afikra, bayan rufe makarantu, da ayyukan gwamnati, an kuma rufe kan iyakokin Liberiya, da Saliyo da kuma Gini. Tuni gwamnatin Liberiya ta ce akwai yuwuwar samun karancin abinci da man fetur bayan kasar Cote d'Ivoire ta haramta wa kasashen da aka samu bullar cutar na Liberiya, da Gini, da Saliyo da kuma Najeriya zuwa tasoshin jiragen ruwan kasar.

Cutar Ebola ta hallaka fiye da mutane dubu a kasashen daga cikin kimanin mutane dubu-biyu da suka harbu da cutar. Hukumar lafiya ta Duniya ta nemi kasashe su daina saka tukunkumin tafiye-tafiye wa kasashen na yammacin Afirka da aka samu barkewar cutar. Najeriya ta tabbatar da cewa mutane 11 a cikin kasar suna dauke da kwayar cutar Ebola, ciki har da wani likita.

Ministan lafiya na kasar Onyebuchi Chukwu ya tabbatar da cewa, akwai mutanen kusan 170 da ake kula da su na yuwuwar ko suna dauke da cutar. Tuni kamfani Aliko Dangote wanda shi ne mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Afirka, ya bayar da gudamawar dala milyan 150 domin dakile cutar ta Ebola.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal