1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS na ƙoƙarin warwware rikicin Mali

November 9, 2012

Ministocin harkokin waje da na tsaro na ƙasashen ƙungiyar gamayyar tattalin arzikin Afirka na zarin sababbin dabarun da suke shirin amfani da su kan 'yan tawayen Mali.

https://p.dw.com/p/16g8K
Hoto: Reuters

Ministocin na gudanar da taron ne a birnin Abuja kafin taron shugabannin ƙungiyar da za a yi ran lahadi ,yanzu haka rikicin na barazanar zamowa rikici mafi girma da tasiri a tsakanin ƙasashen yankin da ke samun goyon baya da ɗaurin gindi na ƙasa da ƙasa da kuma yan tawayen da ke cigaba da mamayar yankin arewacin ƙasar Mali na lokaci mai tsawo.

Abin kuma da yanzu haka ke ɗaukar hankalin ministocin harkokin waje da tsaron ƙasashen yankin yammacin Africa da ke wani taron gaggawa da nufin nazarin dabarun kai soja domin tinkarar rikicin da ake zargi da maida arewacin ƙasar ta Mali wata sabuwar tungar aiyyukan laifi da kuma take hakkin bil adama.

A tsakiyar watan Oktoban da ya gabata ne dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta baiwa ƙasashen yankin kwanaki 45 domin fitar da jadawalin kai soja domin buɗe fafatawar da ɓangarorin ke fatan zata zai kai ga kawo ƙarshen ikon yan tawayen Malin da a cewar Dr Nuradeen Mohammed dake zaman karamin ministan harkokin wajen Tarrayar Nijeria ke buƙatar barin gari ko ta halin kaka.

ECOWAS za ta yanke shawarar tura sojojinta a ƙarshen taron Abuja

Ƙarkashin sabon shirin da ministocin zasu duba tare da miƙa shi ga taron shugabannin ƙasashen yankin a ranar lahadi mai zuwa dai, majiyoyi sun ce ana duban yiwuwar tura aƙalla sojan ƙasashen yankin dubu uku a karon farko.Tuni dai aka fara samun sassauto wa a ɓangaren yan tawayen inda babbar ƙungiyar Ansauradine ta tura wakilanta zuwa ƙasashen Burkina faso da kuma Algeriya domin tattaunawa.Matakin kuma da daga dukkan alamu ya fara faranta ran makwabtan malin da suka zura ido suna ji a jiki sakamakon ayyukan ya'yan ƙungiyar da ƙawayenta.

Burkina Faso Verhandlungen mit Islamisten
Shugabannin ƙungiyar ECOWASHoto: AFP/Getty Images

Ayar tambaya a kan tasirin rundunar sojojin ta ECOWAS a Mali

To sai dai kuma ko ta yaya sabbabin dabarun ka iya kai wa ga biyan buƙatar ƙasa da ƙasa kan Mali dai akwai tsoron yiwuwar tura soja a Malin na iya kaiwa ga ƙazancewar rikicin da ke cikin watansa na bakwai kuma ke samun kwararar sojan ina da jihada daga sassa daban daban na duniya:

ECOWAS-Soldaten Guinea-Bissau
Sojojin ECOWAS a cikin shirin ko takwanaHoto: AFP/Getty Images

Abun kuma da ke iya ƙara ruda harkokin tsaro a yankin da yanzu haka ke ji a jiki sakamakon rikicin kasar Libiya da ke arewa da mali.Abun jira a gani dai na zaman tasirin aiyyukan kwamitin ga kokarin na sake haɗe kasar da tabbatar da zaman lafiyar alummar ta, komi ta ke zama dai lokaci na gaba zai tabbatar mana.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto