1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta cire takunkumi a kan kasar Mali

Abdullahi Tanko Bala
October 6, 2020

Kungiyar raya cigaban tattalin arziki kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta sanar da dage takunkumin da ta kakaba wa kasar Mali bayan da sojoji suka yi juyin mulki a kasar a watan Augusta.

https://p.dw.com/p/3jX4L
Ghana ECOWAS | Nana Akufo-Addo
Hoto: AFP/N. Dennis

A cikin watan sanarwa, kungiyar ta ce shugabannin kasashe da gwamnatoci mambobinta sun yanke shawarar dage takunkumin ne bayan yin la'akari da kyakkyawan mataki da kasar ta dauka na kama hanyar mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya tare da wallafa jadawalin komawa ga mulkin farar hula.

Kungiyar mai mambobin kasashe 15 ta sanya wa kasar Mali takunkumi ne bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita sakamaon zanga zangar gama gari da aka yi ta yi a sassa dama na kasar.

A waje guda kuma an sako madugun adawa a kasar Malin Soumalia Cisse da masu kaifin kishin Islama suka yi garkuwa da shi tsawon watanni shidda yayin yake yakin neman zabe da kuma wata jami'ar agaji ta kasar Faransa wadda ita ma aka yi garkuwa da ita tun shekarar 2016.