1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta yi tir da juyin mulkin soji a Mali

March 22, 2012

Ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta ce ba za ta lamunci matakin soja na kawo ƙarshen demokraɗiyya a Mali ba.

https://p.dw.com/p/14PZf
Renegade Malian soldiers appear on television at the ORTM television studio in Bamako in this March 22, 2012 still image taken from video. Renegade Malian soldiers went on state television on Thursday to declare they had seized power in protest at the government's failure to quell a nomad-led rebellion in the north. REUTERS/Mali TV via Reuters TV (MALI - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS. MALI OUT. NO COMMERCIAL OR EDITORIAL SALES IN MALI
Hoto: Reuters

A martanin sun na farko game da juyin mulkin da ya hamɓarar da gwamantin Amadou Toumani Toure a ƙasar Mali, tarrayar Najeriya da kuma ƙungiyar gamayyar tattalin arzikin ƙasashen yankin yammacin Afika ta ECOWAS sun ce ba za su lamunci matakin sojan na kawo ƙarshen mulkin demokraɗiyyar ƙasar ta Mali ba.

An dai kai ga bugar ƙirji da kiran adabo da duk wani ƙoƙari na juyin mulki, to sai dai kuma ana shirin shan mamaki a yankin yammacin Afirka na ECOWAS da ya wayi gari da wani juyin mulkin sojan da ke zaman ba zata da kuma ya ta da hankula a ciki da wajen yankin.

A Abuja dai ana ci gaba da kartar ƙasar ba'a isa ba kama daga ita kanta hedkwatar hukumar gudanarwar yankin ta ECOWAS da ta ce ba za ta karɓi duk wata gwamantin da ta ƙwaci mulki da ƙarfin hatsi ba, ya zuwa fadar gwamantin Najeriyar da ita ma ta fito ta yi Allah wadai da matakin da shugabanta Goodluck Jonathan ya kira gagarumin ci baya ga demokraɗiyya da mulki na gari a tsakanin ƙasashen.

Rikicin tawayen arewacin Mali ya janyo juyin mulki

Juyin mulkin da ya zo dai dai lokacin da kasar ta Mali ke ƙoƙarin kawo ƙarshen wani tawayen Abzinawa dakea zaman wani babban ƙalubale ga shugabanin ƙasashen yankin 15 da suka share tsawon shekaru kusan biyun da suka gabata suna neman mafita ga jerin rigingimun da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.

Youths protest in front of national television headquarters in Bamako, Mali Thursday, Feb. 2, 2012. Protestors surrounded the palace of Mali's president on Thursday, angry about the government's handling of attacks by Tuareg rebels in the country's north. Protests entered a fourth day Thursday, with demonstrators blocking the streets of the capital, Bamako. (Foto:Moustapha Diallo/AP/dapd)
An jima ana zanga-zangar adawa da rikicin tawaye a MaliHoto: AP

Tuni dai wata tawagar kungiyar ta ECOWAS ta bar Abuja zuwa Bamako domin nazarin halin da ake ciki da kuma sanin mataki na gaba da ya kamaci yayan kungiyar dauka da nufin sake dawo da demokradiyya da mulki na gari

Tuni dai manyan kasashen duniya suka bi sahu wajen tofin ala tsine dama daukar matakin dakatar da dul wani hadin kai da taimako a tsakanin su da kasar da ta dade tana dogaro da agajin turawan yamma domin rayuwa da cigaban alummar ta

Ƙungiyoyin farar hular ƙasashen yankin sun nemi bijirewa sojojin na mali a cewar Dr jibrin Ibrahim dake zaman shugaban kungiyaoyin farar hular kasashen yankin na ECOWAS.

To sai dai kuma ko ya take shirin wanyewa a tsakanin talakawan kasar ta mali da kuma sabbabin mammalakan nasu dai juyin mulkin har ila yau na kara fitowa fili da irin girman barazanar da tasirin rikicin kasar Libya mai makwabtaka da kasashen na ECOWAS ke cigaba da haifarwa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummarsa miliyan 250.

Tasiri Al-Qaida na ƙaruwa a Afirka ta Yamma

Ko bayan juyin mulkin da ake ta'allakawa da galabar da Abzinawan da suka samo makamai da ma ƙwarewar yaki a Libiyan yanzu haka kuma ke riƙe da kusan rabin kasar ta Mali ke samu a gwagwarmayar neman rabon kasar,

Kasashen yankin har ila yau na kuma fuskantar matsalar karuwa da tasirin kungiyar Al-Qaida da kuma yan uwansu na boko haram a tarrayar nigeriar dake zaman mafi girma a yankin.

Mali President Amadou Toumani Toure inspects a Guard of Honor during a ceremonial reception at the Presidential Palace in New Delhi, India, Wednesday, Jan. 11, 2012. (AP Photo/Pankaj Nangia)
Amadou Toumani Toure da sojoji suka yi wa juyin mulkiHoto: AP

An dai share tsawon makon jiya ana shelar neman agajin makamai da kuɗi da nufin taimakawa kasar murƙushe yan tawayen dake rike da fiye da rabin ƙasar ya zuwa yanzu.

Abun jira a gani dai na zaman makomar ƙasar da a baya ake yiwa kallon na kan gaba ga ƙoƙarin tabbatar da demokradiya da mulki na gari a ɗaukacin yankin na ECOWAS.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal