1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da Tunisiya za su yaki ta'addanci

Ahmed SalisuMarch 20, 2015

Kungiyar tarayyar Turai ta EU ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da kasar Tunisiya don yaki da aiyyukan ta'addanci a kasar wanda ke kokarin zama ruwan dare.

https://p.dw.com/p/1Eupc
Unruhen in Tunis
Hoto: picture-alliance/dpa

Kungiyar tarayyar Turai ta EU ta ce wasu daga cikin manyan jami'anta za su je kasar Tunisiya domin nuna goyon bayansu ga yakin da ake da barazana ta ta'addanci da ke kokarin fadada a kasar.

Shugaban EU din Donald Tusk da kantomar hulda da kasashen ketare ta kungiyar Federica Mogherini na daga cikin wadanda za su yi wannan tafiya kuma suka ce tawagar tasu za ta isa kasar ce ranar 31 ga wannan watan.

EU din dai ta ce za ta yi bakin kokarinta wajen yin aiki tare da Tunisiya din da nufin ganin ta'addanci ba samu wurin zama a kasar ba. A makon da ya gabata ne wasu mahara a Tunis suka hallaka mutane 21 wanda galibinsu 'yan yawon bude idanu ne daga kasashen Turai.

Kungiyar nan ta IS da ke rajin kafa daular Islama a Siriya da Iraki dai ta ce ita ce ta ke da alhakin kai harin na birnin Tunis wanda ya gudana a wani gida na dana kayan tarihi.