1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Samar da makoma mai kyau ba Brexit ba

Abdullahi Tanko Bala
April 16, 2019

Shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya bukaci shugabanin kasashen kungiyar su mayar da hankali wajen shata wa kasashen Turan kyakkyawar makoma

https://p.dw.com/p/3GtR5
Belgien Brexit-Gipfel in Brüssel
Hoto: Reuters/Y. Herman

Jean-Claude Juncker ya shaidawa majalisar Turan cewa a yanzu kungiyar tarayyar Turai na iya mayar da hankalinta kan shatawa kanta kyakkyawar makoma kasancewar Birtaniya za ta dauki dogon lokaci kafin ta shawarta ficewa daga kungiyar.

Juncker ya shaiadawa shugabannin kasashe 28 na kungiyar ta EU cewa ficewar Birtaniya ba shine makomar su ba a saboda haka bai kamata batun ficewar ta Birtaniya ta kawo musu wani tsaiko ba.

Ya yi tsokaci kan muhimman abubuwan da ke gaban kungiyar ta suka hada da batun kasafin kudi da cinikayya tsakanin kasa da kasa da kuma zaben sabbin shugabanin kungiyar.