1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafita kan matsalar 'yan gudun hijira a Turai

Abdullahi Tanko Bala SB
June 29, 2018

Shugabannin kungiyar tarayyar Turai sun sanar da samun nasara a karshen taron kolin da suka gudanar na neman mafita kan batun 'yan gudun hijira, matakin da suka ce ya kawo karshen sabani.

https://p.dw.com/p/30Z7q
Italien Symbolbild Rettung von Flüchtlinge
Hoto: Getty Images/AFP/A. Paduano

A taron kolin, shugabannin Turan sun amince da sabon tafarki na yadda za a kula da 'yan gudun hijirar da aka ceto a kan teku. Da farko za a yi kokarin sauke su daga jiragen da suka ceto su sannan a rarraba su ga kasashen da suka amince za su karbe su daga kasashen da suka fara isa kamar Spain da Italiya da kuma Girka, sannan da cibiyoyi da za a samar na tsugunar da 'yan gudun hijirar a arewacin Afirka da kuma yankin Balkans. Sebastian Kurz shugaban gwamnatin Austiriya ya yi bayani inda yake cewa:

"Tattaunawar ta yi tsawo kuma ta yi matukar wuya, to amma na yi farin ciki kasashe da dama a yanzu sun yi matsaya guda wajen rage kwararowar 'yan gudun hijira."

Ita ma dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce ba za bar ya gudun hijira su rinka tsallakawa daga wannan kasa zuwa wata ba tana mai cewa: " Baki daya na yi imanin cewa bayan muhawa mai tsawo kan wannan kalubale mafi girma da ya fuskanci kungiyar Tarayyar Turai, abin farin ciki ne cewa mun cimma manufa ta bai daya. Kuma ina da kwarin gwiwar cewa daga yau za mu ci gaba da aiki domin cike gibin da aka samu a wannan bangare."

A nashi bangaren shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya jaddada nasarar da kasashen Turan suka cimma kan batun na 'yan gudun hijira yana mai cewa: "Wannan sakamako ne na hadin kai da aiki tare. Hadin kan kasashen Turai ya wanzu a kan buri na fifiko kan kasa."

Sai dai kuma a waje daya shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk ya ce nasarar kudirin da shugabannin suka dauka zai tabbata ne idan sun aiwatar da shi kamar yadda aka tsara.