1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta amince da bawa Girka tallafi

December 14, 2012

Kungiyar tarayyar Turai ta amince da bawa Girka tallafin euro miliyan dubu talatin da hudu domin amfani da shi wajen ceto tattalin arzikinta da ya kama hanyar durkushewa.

https://p.dw.com/p/172pr
Hoto: AFP/Getty Images

Shugabannin kungiyar ta tarayyar Turai sun ce sun dau wannan mataki na tallafawa kasar ta Girka da wadanan kudi domin magance masassarar da tattalin arzikin ta ke fama da ita da ma dai bata sukunin cigaba da kansance cikin kungiyar nan ta kasashen Turai da ke amfani da kudin bai daya na euro.

Kazalika kungiyar ta ce ta sake ware wasu kudin da yawansu ya kai euro miliyan dubu 15 da za a ba Girkan tsakanin wannan lokacin zuwa watan Maris mai zuwa duka dai da nufin ganin an kai ga dawo da kasar kan tafarki madaidadaici.

samaras portrait premier athen
Shugaba Antonio Samaras na GirkaHoto: reuters

Baya ga batun agazawa Girka, a hannu guda taron ya amince da girka wata hukuma ta koli da za ta sanya idanu kan bankunan da ke kasashe mambobin kungiyar duka dai da nufi ganin an kai ga yin rigakafi na fadawa cikin matsaloli nan gaba, matakin da masu sanya idanu kan sha'anin tattalin arziki su ka yi na'am da shi.

Amma duk da wannan nasarori da aka cimma, a hannu guda shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce matsalolin da kasashen na Turai ke fama da su ba za su kare ba nan kusa duba da halin da su ka shiga na rashin aikin yi da rashin cigaba da kuma sauye-sauyen da su ka ke yi wanda a cewar ta su na da matukar wahala.

To sai da a nasa bangaren shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya ce an kai ga tushen matsalolin wanda ba karamin cigaba ba ne.

EU Friedensnobelpreis Ehrung Jose Manuel Barroso
Shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel BarrosoHoto: John MacdougalllAFP/Getty Images

Ya ce ''an fuskanci kalubale da dama wannan shekarar musamman ma dai ga kasashen da ke cikin matsala a tsakanin mu amma dai mun gano baki zaren matsalolin da yadda za a magance su. SHa'anin kudi sun dan samu cigaba yanzu kana ana yin gyara game da bangare na kudi''.

Shi ma dai shugaban Faransa Francois Hollande a jawabin da ya yi bayan kammala taron da'awa ya yi ta samun sauki nan gaba musamman ma dai a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Ya ce ''da ya ke za mu gudanar da zabe na kungiyar cikin shekara ta 2014 na majalisar tarayyar Turai wanda zai kai ga kafa sabuwar hukumar zatarswa, kila wannan lokacin ne za mu duba tare da yin gyare-gyare a hukumar ta tarayyar Turai domin samun cigaba''.

Merkel zu Besuch in London mit David Cameron
Angela Merkel da David CameronHoto: Reuters

To baya ga batun tattalin arziki da taron ya fi maida hankai a kai, a hannu guda sun tabo batun rikicin da yanzu haka ake yi tsakanin dakarun shugaba Bashar al-Assad da na 'yan tawaye wanda ke rajin ganin sun kifar da shi daga gadon mulki.

Taron dai ya amince da marawa 'yan tawayen na Siriya baya a fafutukar da su ke inda shugabannin kungiyar su ka bada umarni ga ministocinsu na harkokin wajen su yi amfani da dukannin damar da su ke da ita wajen matsawa shugaba Assad lamba.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan fitowa daga taron, Firaministan Burtaniya David Cameron cewa ya yi ya kyautu kungiyar ta taryyar Turai ta sake duba takunkumi shigar da makamai Siriya da aka girka a baya domin tallafawa 'yan tawayen na Siriya da makamai da sauran kayan aiki a 'yan watanni masu zuwa.

Yayin da Cameron ke wadannan kalamai, a hannu guda takwararsa ta tarayyar Jamus Angela Merkel cewa ta yi ya yi wuri a ce an yi gyara ga dokar ta hana shigar da makamai Siriya duk kuwa da amincewar da ta yi cewar dorewar Siriya za ta kasance ne in har Assad ya kau daga karagar mulki.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Yahouza Sadissou Madobi