EU ta bukaci a sake 'yan jaridu a Myanmar
January 10, 2018Talla
Matakin na kungiyar EU ya zo ne bayan da wata kotu a birnin Yangon ta zargi 'yan jaridun biyu da leken asiri. Hukuncin da kotun ta yanke ta yi amfani da kundin tsarin da ya ba da umarnin daurin shekaru 14 a kurkuku ga masu aikata laifukan leken asirin kasa.
An dai kama Wa Lone da kyaw Soe Oo a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2017 bayan da wasu 'yan sanda biyu suka gayyacesu liyafar cin abinci, sannan suka kwace wasu kundin bayanai. 'Yan jaridun sun soki matakan gwamnatin Myanmar na neman boye gaskiyar al'amarin da ya faru a yakin jihar Rakhine.