1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta gargadi Amirka kan satar bayananta

June 30, 2013

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce in har ta tabbata cewar Amirka na satar bayanan jami'anta da ke ofishinta na Amirka, to tattaunawar da su ke yi ta kasuwaci za ta rushe.

https://p.dw.com/p/18ypD
President Barack Obama, flanked by European Council President Herman Van Rompuy, left, and European Commission President Jose Manuel Barroso speaks to the media, Monday, Nov. 28, 2011, in the Roosevelt Room of the White House Washington. (AP Photo/Haraz N. Ghanbari)
Obama Van Rompuy da BarrosoHoto: dapd

Kwamishiniyar shari'a ta kungiyar Viviane Reding ce ta bayyana hakan a wannan Lahadin, inda ta kara da cewar ba zai yiwu a ce Amirka da kungiyar na tattaunawa kan batu na kasuwaci ba kuma a hannu guda Washington din na satar bayanan wasu daga cikin jami'anta.

Wannan batu dai ya bayyana ne cikin labarun da mullar nan ta Der Spiegel da ake bugawa a kasar Jamus ta wallafa, wadda ta ce ta samu bayanan ne daga cikin irin jerin bayanan sirri na Amirkan na tatsar bayanai ko satar sakonnin imel da Edward Snowden ya kwarmata a kwanakin baya.

Mujallar ta Der Speigel ta ce daga cikin bayanan da ta samu wanda Snowden din ya kwarmata har da wanda ya nuna yadda Amirkan ke tastsar bayanai daga ofishin kungiyar Tarayyar Turai da ke Washington wanda su ka hada da sanya abubuwan jin magana da ma dai satar muhimman takardu na ofishin kungiyar.

Kawo yanzu dai gwamnatin Amirka ba ta ce uffan ba game da wannan batu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman