1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faduwar jirgin habasha ta mamaye jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal MAB
March 15, 2019

Hatsarin jirgin saman kamfanin jiragen saman Habasha wato Ethiopian Airlines da ya auku bayan tashinsa daga birnin Addis Ababa a karshen mako kuma ya halaka dukkan mutane 157 da ke ciki ya dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3F8UO
Äthiopien Flugzeugabsturz Ethiopian Airlines Flight ET 302
Hoto: Reuters/T. Negeri

 

Idan muka fara da jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi: kuskure a tsarin na'urar sarrafa jirgin sama, sai ta ci gaba tana mai cewa: Hatsarin jirgin saman nan samfurin Airbus 737 Max 8 ya shafi kamfanin Ethiopian Airlines da ke iya kokarin taka rawa a fagen sufurin jirgin sama na kasa da kasa. Kamfanin na da kyakkyawan suna a gun masana harkar sufurin jirgin sama da ma fasinjoji, wasu jaridun duniya ma na yi wa kamfanin taken „Tauraron sufurin jirgin sama a Afirka.

Sai dai jaridar ta Süddeutsche Zeitung ta ce darasin da za a dauka daga hatsarin na karshen mako shi ne kamfanonin kera jiragen sama ba su yi tunani mai zurfi ba kan sakamakon kirkiro sabuwar fasahar da jirgi ke iya sarrafa kanshi da kanshi ba. Dole ne su zuba makudan kudade wajen horas da matukan jiragen sama sabbin fasahohin, su kuma yi watsi da tsohon tsarin ba da horo. Dole ne matuka jirgin sama da injiniyoyi su kara samun fahimtar sabbin tsare-tsare masu daure kai.

Ita kuwa a sharhin da ta yi dangane da hatsarin jirgin saman, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara da cewa matukan jirgin sama na korafi game da jirgin saman Boeing. Ta ce tun bayan hatsarin jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines a ranar Lahadi da ta gabata, kamfanin kera jiragen sama na Boeing ya shiga tsaka mai wuya, inda tuni ma kamfanonin  jiragen sama da dama da ke amfani da samfurin Boeing 737 Max 8 suka dakatar da aiki da jiragen a wani mataki da za a iya bayyana shi da cewa idan ka ga gemun dan uwanka ya kama da wuta to shafa ma naka ruwa.

Kotu ta dakile koken wasu kabilun Namibiya

USA Justiz l US-Richterin verwirft Klage namibischer Volksgruppen Herero und Nama
Hoto: Getty Images/AFP/D. Emmert

  Wata kotu a birnin New York na kasar Amirka ta yi watsi da karar da kabilun Herero da Nama na kasar Namibiya suka shigar don neman a tilastawa gwamnatin Jamus biyan diyya ta miliyoyin dubbai bisa kisan kare dangi da 'yan mulkin mallakar jamus suka aikata a Namibiya tsakanin shekarar 1904 zuwa 1908 in ji jardar Neues Deutschland. Jaridar ta ce a wancan lokaci na mulkin mallaka dakarun Jamus sun murkushe masu tada kayar baya, sannan sun aikata kisan kare dangi a kan kabilun Herero da Nama da aka kiyasta ya yi sanadin mutuwar mutum kimanin dubu 100.

Ko da yake bayan kai ruwa rana gwamnatin Jamus ta ce an aikata kisan kare dangi amma ta ki neman gafara daga wadanda abin ya shafa don kauce wa biyan diyya, yanzu kuma ta samu goyon baya daga kotun ta birnin New York, abin da ke zama babban koma baya ga yunkurin kabilun Herero da Nama na ganin an ba su hakkinsu. Sai dai duk da wannan hukunci akwai yiwuwar daukaka kara, inji jaridar.