1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar Jamus game da neman dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu na MDD

July 22, 2004

Tun a farkon shekarun 1990 ne Jamus ta fara tunanin neman dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu na MDD bayan sake hadewar kasar karkashin tuta guda da kuma rawar da shiga takawa a ayyukan kiyaye zaman lafiyar na MDD.

https://p.dw.com/p/Bvhr

Jamus a shirye take ta dauki karin nauyi kanta a kwamitin sulhu na MDD, kamar yadda aka ji daga shugaban gwamnati Gerhard Schröder, lokacin da yake jawabi ga babbar mashawartar majalisar a cikin watan satumban bara, inda ya kara da cewar:

Ina goyan bayan ra’ayin sakatare-janar a game da cewar kwamitin sulhu ba zai cancanci amsa wannan suna ba sai idan ya kasance yana da wakilci dukkan yankunan duniya. Wajibi ne a aiwatar da garambawul da kuma shigar da karin kasashe domin kwamitin ya kunshi kasashe masu tasowa. Dangane da Jamus kuwa, ba zan dadara ba ina mai nanata cewar kasar a shirye take da dauki karin nauyi kanta a karkashin irin wannan mataki na garambawul.

Ko da yake tun a farkon shekarun 1990 ne kasar ta Jamus ta fara bayyana sha’awarta ta samun dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu na MDD bayan sake hadewar yankunan gabaci da yammacin Jamus. Amma an sake farfado da wannan fafutukar ne lokacin da sakatare-janar Kofi Annan ya sake tabo maganar garambawul ga tsare-tsaren MDD a shekarar da ta wuce. Wani kwamitin rikon kwarya da aka nada shi ne ke bitar manufofin na garambawul, wanda za a gabatar ga Kofi Annan shekara mai zuwa. Wannan manufar ita ce ta ba wa shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya fito fili yana mai bayyana bukatar Jamus a cikin watan maris da ya wuce, inda yake cewar:

Wajibi ne kasashen dake taka muhimmiyar rawa a nahiyar Afurka da Asiya da Latin Amurka su samu dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu. Wannan maganar, kazalika ta hada har da kasashe masu ci gaban masana’antu, wadanda ke ba da kakkarfar gudummawa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya. Ta la’akari da haka ita ma Jamus ta shiga rukunin kasashen dake neman dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu na MDDr.

Hujjar kasar a game da haka shi ne kasancewarta ta uku a tsakanin kasashen dake ba da gudummawa mafi tsoka ga kasafin kudin majalisar da kuma rawar da take takawa a matakan kiyaye zaman lafiya fiye da kasashe masu yawan gaske. Kasar kazalika ta samu daukaka a idanun duniya dangane da cikakken goyan bayan da ta ba wa kudurorin MDD a game da yakin Iraki. Amma fa a nan ne take kasa tana dabo, saboda mai yiwuwa Amurka ta haye kujerar na ki sakamakon adawar da Jamus ta nuna akan yakin kasar ta Iraki. Shi dai Kofi Annan yana kan bakansa na garambawul ga tsare-tsaren MDDr nan da shekara ta 2007 lokacin da wa’adin shugabancinsa zai zo karshensa. Shawarar da aka gabatar dai shi ne shigar da karin kasashe biyar a kwamitin sulhun, wadanda zasu hada da wata kasa ta Afurka da kuma daya daga Asiya sai daya daga Latin Amurka da kuma wasu guda biyu daga kasashe masu ci gaban masana’antu. A baya ga Jamus kuwa akwai kasar Japan, wacce ita ma take neman wakilci na dindindin a kwamitin sulhun na MDD.