1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar kare hakkin 'yan gudun hijira

Stefanie Duckstein/ YBAugust 26, 2015

Meron Estefanos 'yar jarida ce daga kasar Eritrea, kana 'yar fafutuka ce da yanzu haka ta ke zaune a Sweden. Ta shafe tsawon shekaru wajen nemawa 'yan gudun hijira hakkinsu.

https://p.dw.com/p/1GLiG
Menschenrechtsaktivistin Meron Estefanos
Hoto: DW/Meron Estefanos

Da wuya Meron Estefanos ta iya rayuwa ba tare da wayar salularta ba. Rayuwarta ta karkata ga yin fafutuka. Ta kan kasance cikin yin bayanin abinda ke faruwa.

A wajen wani taron Freedom Forum a birnin Oslo shugabanni da wanda suka karbi kyautar Nobel ne za su yi jawabai.

Estefanos ta kasance cikin wadanda ke wajen kuma za ta yi jawabi kan yakin da ake yi da mulkin danniya da hakkin 'yan gudun hijira.

"Idan aka kira ni daga Libiya ko Masar ko Isra'ila ko wani wajen, muna da wakilan gwamnatin Eritrea da ya kamata su taimaka musu amma kuma gwamnatinmu ba ta sauraronsu. Masu fafutuka iri na ne ke yin irin aikin da ya kamata a ce jakada ya yi."

Meron Estefanos ta shafe shekaru uku tana jiran wannan lokacin.

Meron Estefanos da 'yan gudun hijira daga Eritrea
Hoto: privat

Yanzu haka za ta hadu da dan kasarsu Estifanos Tsehaye. Mutumin dan shekaru 19 ya samu damar shiga Turai.

Tsehaye ya bar Eritrea cikin shekarar 2012 don guje wa gwamnatin kama karya da azabtarwar da take wa mutane gami da barazanar kisa. Tsehaye ya ce ba irin wannan rayuwar yake son yi ba.

Wasu mutane ne suka kama shi a Masar kana suka daure shi a wani sansani da suka ware don azabtar da mutane.

"Na ga bala'in da ban taba gani ba. Su kan kona mutum ko su yi maka azaba da lantarki. Zalunci na da yawa. Ba na ma son tuna abubuwan."

Meron Estefanos kan dauki hotuna da kuma adana bayanai na irin wannan azabtarwar. Takan rubuta sunan wanda aka azabtar da na 'yan uwansa kuma ita ke karbo kudaden fansa.

Meron Estefanos da 'yan gudun hijira daga Eritrea
Hoto: privat

Wanda suka kame Tsehaye ga misali sun karbi kudin fansa har Euro dubu 20 kafin su sake shi. Daga nan ne ya tafi Libiya da Italiya kafin ya shiga Norway.

Wannan aiki dai ya sanya Estefanos zuwa kasashen duniya da dama kamar Isra'ila da Sudan da kuma Amirka. Ta nemi masaniya ta hanyar da 'yan gudun hijira ke bi sannan ta san lokacin da jiragen Turai ke barin Libiya.

A Stockholm ne 'yar jaridar mai shekaru 40 ke tattara bayanan matsalolin 'yan gudun hijira a duniya.

Wata 'yar Eritrea da ke cikin matsala ta bugo mata waya. Matar ta samu kubuta daga hannun wanda suka sace ta amma yanzu ta makale a Sudan.

Meron Estefanos na gabatar da shiri a tashar Radio Erena. Tashar na watsa shirye-shiryenta ga 'yan Eritrea kuma ta nan ne suke samun labarin halin da 'yan uwansu ke ciki.

"Akalla ga iyalan mutanen da suka bace, mu kan shaida musu ko mutum ya rasu ko kuma yana raye. Wannan babban abu ne gare su."

Yaki da gwamnatin kama karya abu ne mai wahala inji Estefanos amma a cewarta manyan gwaraza, su ne 'yan gudun hijira.