1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falasdinu na son zama mamba a kotun ICC

Ahmed SalisuJanuary 2, 2015

Mahukuntan Falasdinu sun mika takardunsu ga Majalisar Dinkin Duniya na neman izinin zama guda daga cikin mambobi na kotun hukunta laifukan yaki ta kasa da kasa ta ICC.

https://p.dw.com/p/1EEPf
UN Vollversammlung 26.09.2014 - Mahmud Abbas
Hoto: Reuters/Mike Segar

Jakadan Faladinu a zauren Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ne ya mika wadannan takardu a Juma'ar nan a mastayin matakin samun rijista na shiga kotun wanda zai bata damar neman a gurfanar da kowacce kasa da ta ke zargi da aikata mata laifukan yaki.

Wannan matakin na Falasdinu dai na zuwa ne bayan da ta gaza samun goyon baya na kasancewa kasa mai cikakken iko a wata kuri'a da aka kada a Majalisar Dinkin Duniya.

Tuni dai Izra'ila da ke zaman doya da manja da Falasdinu ta nuna rashin amincewarta da matakin Faladinun na shiga kotun, inda ta ke cewar za ta maida martani kakkausa muddin Falasdinu ta shiga kotun.