1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Fara kasuwanci maras shinge tsakanin kasashen Afirka

May 30, 2019

Yarjejeniyar cinikayya maras shinge tsakanin kasashen Afirka. Kasashe 44 suka sanya hannu kan yarjejeniyar. Sai dai Najeriya da wasu kasashen nahiyar sun kaurace, lamarin da ake gani zai rage tasirin shirin.

https://p.dw.com/p/3JVLE
Ruanda Kigali Unterzeichnung Afrikanisches Freihandelsabkommen
Hoto: Getty Images/AFP/STR

 

 A Taron koli na shugabannin kasashen Afirka karo na 18 da ya gudana a birnin Adis Ababa na kasar Habasha  a watan Janerun 2012 ne, shugabannin nahiyar suka fito da wannan shiri na kafa wata kungiyar kasuwanci maras shinge ta African Continental Free Trade Agreement  AfCFTA a takaice ko kuma ZLEC wato zone de libre-échange continentale a Faransance da za ta hade a wuri daya illahirin kungiyoyin tattalin arzikin na yankunan dabam-dabam na nahiyar Afirka irinsu ECOWAS/CEDEAO daga Afirka ta Yamma, SADC daga kasashen Kudancin Afirka da dai sauransu, ta yadda jama'a daga illahirin kasashe 55 na nahiyar Afirka za su iya shigi da fici su da dukiyoyinsu ba tare da fuskantar wani tarnaki ba.

Matakin da zai taimaka ga fitar da kasashen nahiyar baki daya daga kangin talauci da ma kuma samun karfin fada a ji a tsarin hada-hadar kasuwanci a duniya. A shekara ta 2018 a taron koli na shugabannin Afirka da ya gudana a birnin Kigalin kasar Ruwanda kasashe 44 sun sanya hannu kan wannan yarjejejniya a bisa manufa.

Ruanda Kigali Unterzeichnung Afrikanisches Freihandelsabkommen
Hoto: picture-alliance/Xinhua/G. Dusabe

Wannan kasuwar hadaka ta Afirka wacce ta kunshi mutane kimanin miliyan dubu da 500 za ta taimaka ga samar da ayyukan yi a nahiyar.  To sai dai duk da kyakkyawan fata da ke tattare da wannan wagegeyar kasuwa ta tsakanin 'yan Afirka, shirin na da kalubalai masu yawa.

Wasu daga cikin matakan da suka rage ga wannan shirin kasuwancin maras shinge tsakanin kasashen Afirka shi ne kafa hukumar saka ido da tsarin kasuwancin da kuma warware rigingimun cinikayyan da ka iya tasowa da ma uwa uba hanyoyin samar da kudaden aiwatar da wannan kungiya wacce idan dai har ta girku to kuwa za ta kasancewa kungiyar kasuwanci mafi girma a duniya a fannin yawan jama'a da kuma kasashe.