1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: An jima ana shiri kafin harin Nice

July 21, 2016

Tuni dai mahukunta a kasar suka tsare mutane biyar da ake zargi sun tallafa wa Bouhlel da ya kaddamar da harin na ta'addanci ta hanyar amfani da bababar mota a birnin na Nice.

https://p.dw.com/p/1JTvr
Trauer um Opfer in Nizza
'Yan ta'adda dai na sanya jimami a rayuwar 'yan uwan mamatan saboda rashin imaniHoto: Reuters/P. Rossignol

Mai gabatar da kara a Faransa Francois Molins ya bayyana a ranar Alhamisd din nan cewa wanda ya kai harin nan a birnin Nice a bikin ranar 'yanci Mohamed Lahouaiej Bouhlel ya samu taimako kafin ya kaddamar da harin da ya aikata ta hanyar amfani da babbar mota ya tattake jama'a.

Tuni dai mahukunta a kasar suka tsare mutane biyar da ake zargi sun tallafa wa Bouhlel da ya kaddamar da harin na ta'addanci a birnin na Nice.

Molins ya ce mutane biyar cikinsu maza hudu da mace guda akwai hannunsu a harin da suka dauki watanni suna kitsa yadda za su kai shi.

Masu bincike sama da 400 ne suka shiga aiki kan shedun binciken harin tun daga ranar 14 ga watan Yuli inda Bouhlel ya kaddamar da harin rashin imani kan jama'a da ya halaka 84 da raunata wasu 400.

Za dai da tuhumi mutanen da suka tallafa wa Bouhlel da laifin hada baki a aiwatar da ayyukan ta'addanci ban da wasu laifuka.