1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A karo na biyu Faransa ta dauki kofin kwallon kafa ta duniya

Abdullahi Tanko Bala
July 15, 2018

Faransa ta dauki kofin kwallon kafa ta duniya na 2018 bayan lallasa kasar Croatia da ci 4-2 a wasan karshe da aka buga a birnin Moscow

https://p.dw.com/p/31VB0
Russland WM 2018 Frankreich gegen Kroatien
'Yan wasan kwallon kafar Faransa suna murnar lashe kofin duniyaHoto: REUTERS

Faransa ta lashe gasar kofin kwallon kafa ta duniya na 2018 bayan da ta doke Croatia da ci 4-2 a wasan karshe da aka buga da maraicen yau Lahadi a birnin Moscow. Wannan dai shine karo na biyu da Faransar ta dauki kofin kwallon kafar na duniya, ta dai dauki kofin a shekarar 1998.
Ga kasar ta Faransa wannan nasara ce ta kwazo da himma da 'yan wasanta suka nuna a gasar ta Rasha, kuma zakaran gwajin dafi ne na yan wasanta sabbin jini wadanda suka taka rawar gani.

Russland WM 2018 Frankreich gegen Kroatien
'Yan wasan kwallon kafar Faransa suna murnar lashe kofin duniyaHoto: REUTERS

Ita ma Croatia wannan ne karon farko da ta kai zagayen karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.