1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Faransa ta goyi bayan zaben Alassane Ouattara

November 20, 2020

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya goyi bayan sake zaben Shugaba Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasar Côte d'Ivoire karo na uku.

https://p.dw.com/p/3ldNj
Elfenbeinküste Abidjan | Alassane Ouattara, Präsident & Emmanuel Macron, Präsident Frankreich
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/C. Bah

A cikin wata hira da ya yi da mujallar Jeune Afrique Emmanuel Macron ya ce mutuwar da dan takarar jam'iyya mai mulki ya yi dab da zaben na Côte d'Ivoire shi ne a fahimtarsa dalili kwakkwara da ya sa babu wani zabi da ya ragewa Alassane Ouattara in ba ya tsaya takara ba. 

Mr. Macron ya ce yana baya-baya da magana kan batun domin yana son sauya yadda ake ganin Faransa na tsoma baki a siyasar kasashen da ta yi wa mulkin mallaka. To amma duk da haka ya ce zai yi kyau idan Shugaba Ouattara ya bude kofofin tattaunawa da jiga-jigan masu adawa da shi ciki kuwa har da tsohon shugaba Laurent  Gbagbo.