1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta fara kwashe jama'arta daga Haiti

March 24, 2024

Kasar Faransa ta ce za ta samar da jiragen sama na mussaman da za su yi jigilar kwashe 'yan kasar ta masu rauni daga kasar Haiti.

https://p.dw.com/p/4e4hv
Faransa za ta fara kwashe jama'arta daga Haiti
Faransa za ta fara kwashe jama'arta daga HaitiHoto: Guerinault Louis/Anadolu/picture alliance

Ma'aikatar harkokin waje ta Paris ta ce za ta fara kwashe jama'arta daga Haiti yayin da aka katse jigilar jiragen sama ta birnin Port-au-Prince a lokacin da aka samu barkewar rikicin siyasa. Sai dai kuma offishin jakadancin Faransa a birnin zai ci gaba da aiki duk da halin zaman dar-dar da ake ciki.

Karin bayani: Firaministan Haiti ya yi murabus daga mukaminsa

A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Faransar ta fitar, ta ce, an aje ma'aikata ne a offishin jakadancin domin su taimakawa Faransawa da ke kasar.

Alkalumma sun yi nuni da cewa, kimanin Faransawa 1,100 ne suke zaune a Haiti. Tun dai a farko watan Fabarairun wannan shekarar ce dai rikci ya barke a birinin na Port-au-Prince wanda ya yi sanadiyar murabus din Firanministan kasar Ariel Henry. Sai dai har yanzu kura ba ta gama lafawa ba duk da cika bukatar gungun kungiyoyi masu dauke da makamai da Firanminstan ya yi, inda a yanzu suke rike da ikon kaso mafi girma na birnin.