1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar amfani da miyagun makami a lardin Idlib

Mahmud Yaya Azare MA
September 14, 2018

Yayin da bangarorin da ke rikici a Siriya ke kara jan damarar samun iko a Idlib, ana ci gaba da nuna fargabar yin amfani da makamai masu guba kan lardin da ke dauke da miliyoyin mutane.

https://p.dw.com/p/34swG
Munster - Vernichtung von chemischen Waffen GEKA
Hoto: Nigel Treblin/Getty Images

Kasashen Rasha da Siriya da Iran na daf da kaddamar da farmakin ayita ta kare a kan birnin, lamarin da ke zuwa mako guda bayan wargajewar zaman sulhu kan yankin Idlib da aka yi a birnin Tehran na Iran. Ministan tsaron Turkiya Hulusi Akar, ya ce kasarsa ba za ta nade hannu a yi mata tsakiyar da babu ruwa ba.

“Halin da ake ciki a Siriya yana barazana ga tsaronmu da ma tsaron dukkanin duniya. Duk wani hari kan lardin Idlib zai iya kara kwararar 'yan gudun hijirar da a yanzu ma sun fi miliyan uku cikin kasarmu. Ban ga dalilin da za a ce ba za a dauki matakan hana aukuwar wannan matsalar ba, sai bayan an yi amfani da makamai masu guba a madadin daukar matakan riga kafin da za su rage asarar rayuka da dukiyoyi”
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Siriya, Steffan de Mistura, shi ma ga dukkan alamu kamar sauran kasashen yamma, damuwarsa ba murkushe 'yan ta'addan da ke cikin birnin bane, muddin dai ba za a yi amfani da makamai masu guba ba.

Schweiz UN Friedensgespräche für Syrien
Hoto: picture-alliance/Photoshot/Xu Jinquan

 

Tuni dai shugaban kungiyar Annusra, Abu Muhammad al-Julani, ya sha alwashin gwabza yaki har bakin ransu:

“Da zarar ka yi tunanin mika wuya ga makiyi ko mika makaminka, to alal hakika, ka ci amanar Allah da Manzonsa, da ‘yan uwanka da suka kwanta dama, da tsararru da wadanda aka raba su da gidajensu”

Koda yake duk da wanan kurari na Julani, kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, manyan kwamandojin 'yan ta'addan sun tsere daga yankin tun cikin 'yan makonnin da suka gabata, da sunan tafiya aikin hajji, kamar yadda kuma wasu suke ta samun hanyoyi suna komawa kasashensu .

Koma dai ya za ta kaya, irin yadda kowane bangare ke kada gangar yaki ya sanya masharhanata , irin su Abdul Bari Atwan, ke nuna mummunar fata ga makomar birnin na Idlib.