1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar barkewar corona a Najeriya

July 18, 2021

Kwamitin shugaban kasa kan yaki da annobar corona a Tarayyar Najeriya, ya ware jihohi shida da babban birnin kasar a matsayin yankuna mafiya hadari da ake fargabar barkewar cutar zagaye na uku.

https://p.dw.com/p/3wewZ
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Jihohin sun hada da  Lagos da Oyo da Rivers da Kaduna da Kano da Plateau da kuma Abuja fadar gwamnatin kasar. Mai magana da yawun shugaban kwamitin Willy Bassey ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa, hakan na nufin kara tsaurara matakan hana yaduwar cutar musamman a wannan lokacin da ake fama da sabon nau'inta samfurin Delta.

Wannan gargadin dai na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmin kasar ke shirye-shiryen gudanar da shagulgulan Babbar Sallah.