1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai matsalar abinci a Sudan ta Kudu

Abdul-raheem Hassan
September 13, 2021

Hukumar abinci ta duniya za ta dakatar da shirin samar da abinci ga mutane akalla 100,000 da suka rasa muhallansu a kasar Sudan ta Kudu, sakamakon karancin kudaden gudanarwa da ta ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/40GHq
Sudan Symbolbild Wirtschaftskrise
Hoto: Simon Wohlfahrt/AFP

Matakin zai fara ne daga watan Nuwamban 2020 har zuwa watan Janairun 2022, an kiyasta mutane 106,000 da ke zaune a Juba babban binrin kasar za su shiga wani hali, sanna matsalar yunwan zai shafi mutane masu yawa a sauran sassan kasar da hukumar WFP ke gudanar da aikin agaji a Sudan ta Kudu.

Sanarwar na zuwa ne jim kadan bayan da hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ta bayar da rahoton cewa ambaliyar ruwa ta shafi mutane 380,000 gonaki sun lalace, gidaje da dama sun rushe, matakin ya tilas da mutane da dama sun rasa matsugunansu a cikin kasar da ke fama da talauci.