1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar sake aukuwar rikici bayan zaben Kenya

March 8, 2013

Duk da matsalolin da aka fuskanta wajen tattara sakamakon zaben shugaban kasar Kenya, masu sa ido a zabe sun yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali.

https://p.dw.com/p/17tm8
People gather to discuss the presidential elections results at the Kondele neighbourhood in the western town of Kisumu, 350km (218 miles) from the capital Nairobi, March 7, 2013. The running mate of Kenya's presidential candidate Raila Odinga called for the vote count to be halted on Thursday and cast doubt on the fairness of a process that is still incomplete three days after the poll, remarks that could inflame a largely peaceful election. REUTERS/Thomas Mukoya (KENYA - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan zaben kasar Kenya. A rahotonta jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne kamar haka: Zullumi na dakon sakamakon zabe a birnin Nairobi sannan sai ta ci-gaba da cewa.

"Yayin da aka samu jinkiri wajen kidayar kuri'u a zaben kasar Kenya, ana kara samun fargabar yiwuwar sake aukuwar wani rikici. A wani mataki na rigakafi, 'yan sanda na yin sintiri musamman a unguwannin marasa galihu dake gabacin Nairobi babban kasar, inda tun a tsakiyar mako komai ya tsaya cik ba ka ganin mutane a kan tituna, yayin da kantuna da makarantu suka kasance a rufe. Da farko dai hukumar zaben kasar ta so ayyana sakamakon zaben shugaban kasa a ranar Laraba, amma an samu jinkirin kidayar kuri'u, kuma ya kara sanya fargabar cewa ana iya sake samun aukuwar tashe tashen hankulan da suka biyo bayan zaben kasar na karshen shekarar 2007. Sai dai duk tangardar na'urar zabe da aka fuskanta, amsu sanya ido a zabe sun yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana."

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci a kan zaben na Kenya inda ta ce:

Überschrift: Vote counting in Kenyan elections (PIC 4.JPG) Schlagworte: Kenyan elections 2013, Wer hat das Bild gemacht: James Shimanyula Wann und wo wurde es aufgenommen: Nairobi, Kenya, 06.03.2013 Was ist darauf zu sehen: Security  men  patrolling  a  section  of  Bomas  of  Kenya,  the  main  national  Vote  Tallying  center  on  the  outskirts  of  the  Kenyan  capital  Nairobi. James Shimanulya ist DW Korrespondent.
Hoto: DW/J.Shimanulya

"Matsalolin fasaha sun jinkirta ba da sakamakon zabe, abin da ya janyo kace nace game da aikin kidayar kuri'u, musamman shawarar da shugaban hukumar zabe Issac Hassan ya yanke ta shigar dukkan kuri'un da aka kada cikin lissafi wato har da wadanda suka lalace. Jaridar ta ce bambamtawa tsakanin kuri'un da  aka kada da wadanda suke sahihai yana da wahala, domin kuri'un da da yawa daga cikin 'yan kasar ta Kenya suka jefa sun lalace kasancewar ba su fahimci sabon tsarin zaben kasar ba."

Tabarbarewar harkar ilimi a Najeriya

Ita kuwa jarida die Tageszeitung tsokaci ta yi a kan harkar ilimi a tarayyar Najeriya tana mai cewa, mai za faru idan malamin firamare ya fadi a jarrabawar makarantun firamare? Ta ce a jihar Kaduna kashi uku cikin hudu na malamai sun fadi a jarrabawar karshe da ake wa 'yan aji hudu na firamare. Kamata yayi wadannan malaman sun lakanci matakin farko na lissafi da rubutu da kuma 'yar masaniya ta adabin Najeriya. Jaridar ta ce abin bai ba da mamaki ba domin a karshen watan Nuwamban bara, an gano malamai kimanin 2000 a Najeriya dauke da takardun shahada na bogi, sannan rabinsu ba su da kwarewar koyarwa a makaranta. Ta ce a da Najeriya na zaman jagaba a harkar ilimi a yammacin Afirka, amma yanzu harkar ilimi a kasar ta koma-baya."

Eine junge muslimische Lehrerin steht am Dienstag (20.09.2005) in einer Schule in den Bergen nördlich von Abuja, der Hauptstadt des westafrikanischen Staates Nigeria, im Klassenzimmer an der Tafel. Foto: Wolfgang Langenstrassen +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Rashin ba wa fararen hula kariya a rikicin Kongo

Fararen hula ba sa samun kariya a fagen daga, har wa yau dai inji jaridar ta die Tageszeitung ta na mai nuni da halin da ake ciki a kasar Kongo, inda ta ce daruruwan mutane sun rasu a gumurzun da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da sojojin sa kai a wani yanki dake gabas da Kinshasa babban birnin kasar. Sojojin Majalisar Dinkin Duniya da aka girke a yankin don ba da kariya, sun kasa yin wani abin kirki na hana wannan ta'asar aukuwa. A wasu lokutan ma ana zargin su da korar wadanda lamarin ya shafa zuwa gidajensu.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar