1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar tsanantar annobar cutar Ebola

September 3, 2014

Kungiyar Lafiya ta Duniya da kungiyar agajin kiwon lafiya ta Medicines sans Frontiers sun yi gargadin cewar annobar cutar nan ta Ebola ka iya tsananta kafin a kai ga shawo kanta.

https://p.dw.com/p/1D5kt
Ebola Seuche Afrika Helfer
Hoto: D.Faget /AFP/Getty Images

Dr. Joanne Liu da ke zaman shugabar kungiyar Medicines sans Frontiers ta ce alamu na nuna cewar hukumomin kiwon lafiya da kasashe na neman gazawa a yakin da ake da cutar, inda ta kara da cewar a yammacin Afirka ana samun karuwar wanda ke kamuwa da cutar da ma wanda cutar ta hallaka yayin da jami'an kiwon lafiya da ke jinyar masu cutar su ma ke kamuwa da ita kuma da damansu ke rasuwa wanda hakan ya sanya wasu jami'an na kiwon lafiya tserewa daga bakin aiki, lamarin da ya sanya ake barin masu wannan larura cikin wani hali.

Cutar Ebola dai yanzu haka ta yi sanadin rasuwar mutane kimanin dubu da dari biyar a Gini da Liberiya da Saliyo da kuma Najeriya wadda ke zaman kasa ta baya-bayan nan a yammacin Afirka da cutar ta bulla.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu