An gudanar da kuri'ar jin ra'ayi a Faransa
January 25, 2019Talla
Sama da watanni biyu ke nan da wasu daga cikin al'ummar kasar suka fara tawaye a sakamakon karin kudin harajin mai a kasar, jagororin zanga-zangar sun umurci magoya baya da su fito don ci gaba da zanga-zangar, kusan mutane dubu 84 ne suka gudanar da zanga-zangar a karshen makon daya gabata. Sai dai wani sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a, ya tabbatar da karuwar farin jinin shugaban kasar tsakanin al'umma yayin da yake ci gaba da rangadi a bangarorin kasar.