1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmakin soke a kan 'yan aware a Slaviansk

May 2, 2014

Dakarun Ukriane sun kaddamar da samame domin murkushe 'yan aware da suka kakkabi jirgin gwamnati a Slaviansk da ke gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/1Bt3g
Hoto: Reuters

Sojojin gwamnatin Ukraine sun kaddamar da farmakin a kan 'yan aware da ke goyon bayan Rasha, domin kawo karshen mamaye wasu muhiman wurare da suke yi a birnin Slaviansk da ke gabashin kasar. Wannan dai martani ga matakin da 'yan a waren suka dauka na harbe jirgin saman gwamnati, inda suka hallaka sojoji biyu, yayin da su ma a bangarensu a ka samu mace-mace.

Ministan cikin gidan wannan kasa Arsen Awakow ya ce dakarun gwamnati sun kwace iko wuraren da dama ya zuwa yanzu ciki kuwa har da babbar tashar jirgin kasa na Slaviansk. Sannan kuma tashar telebijin na wannan birni ta na karkashin ikon sojojin gwamnati. Tun dai makwani biyun da suka gabata ne masu rajin ballewa da ke goyon baya Rasha suka mamaye muhimman gine-ginen Slaviansk.

Sai dai kuma a daya hannu yanzu haka a birnin Luhansk masu rajin ballewa sun sasanta da hukumomin yankin, inda don radin kansu suka fice daga tashar telebijin da kuma ofishin babban mai shigar da kara da suka mamaye.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nassiru Awal