Firaministan Lesotho ya sauka daga mukaminsa
May 19, 2020Murabus din Thabane na zuwa ne bayan watanni uku da 'yan sanda suka ambaci sunansa da shi matarsa a cikin wani laifin kisan kai da aka aikata a kasar da ke kusa da Afirka ta Kudu. Tun farko 'yan sanda sun zarge shi da hada baki da matarsa ta yanzu wurin kisan tsohuwar matarsa, a shekara ta 2017, kwana biyu bayan ya dare kujerar Firaminista. Lamarin dai ya haifar da zazzafar muhawara a kasar.
An kuma ta matsa mi shi lamba a kan wannan zargi ta kowane bangare. Sai dai a jawabin da ya yi wa 'yan Lesotho a wannan Talata koda sau daya bai ambaci batun kisan kan da ake zarginsa da aikatawa ba.
''Ya 'yan uwana 'yan Lesotho na tsaya yau a gabanku don in sanar da ku cewa watakila ban kammala aikin da kuka dora a kafadata ba, amma lokaci ya yi da zan janye jigi daga harkar shugabanci . Ina rokon ku da ku ba wanda zai gajeni goyon baya yadda ya kamata.'' inji tsohon firaministan.
An sanar da nadin Ministan Kudin kasar Dr Moeketsi Majoro a matsayin sabon Firaministan kasar ta Lesotho.