1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabar kasar Taiwan za ta nada sabon Firimiya

Zulaiha Abubakar
January 10, 2019

Sakamakon rashin nasarar jam'iyya mai mulki a zaben yankunan da ya gudana a kasar Taiwan Firimiyan kasar William Lai ya bayyana cewar zai sauka daga mukaminsa tare da majalisar zartaswa.

https://p.dw.com/p/3BJKS
William Lai
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Lai

Wannan rashin nasarar zabe dai na barazana ga shugabar kasar Tsai Ing-wen, wacce a halin yanzu ke fuskantar suka sakamakon sabbin matakan kawo sauyin da ta kaddamar a kasar, a daidai lokacin da kasar China ke ayyana Tsibirin a matsayin mallakinta. Shugabar kasar wacce jam'iyyar ta, ta sha kaye ta shirya tsaf don sanar da sabon firimiya. A farkon wannan wata ne shugaba Xi Jinping  na kasar China ya sake waiwayen aniyarsa ta amfani da karfin soja don mayar da Taiwan karkashin mulkin China. Tun bayan darewar shugaba Tsai Ing-wen mulkin kasar Taiwan a shekarar ta 2016, kasar ke fuskantar barazana daga shugaba Xi Jinping na Kasar China, wace ta ke daukar Taiwan a matsayin wani bangaren kasar da ya yi tawaye.