1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fito na Fito tsakanin jami´an tsaro da ´yan adawa a Rasha

November 25, 2007
https://p.dw.com/p/CSrf
Mako guda gabanin zaɓen ´yan majalisar dokoki da zai gudana a Rasha an tsaurara matakai kan ´yan adawa. A gun wani taron gangamin yiwa shugaba Vladmir Putin tofin Allah tsine a birnin Mosko, ´yan sanda sun kame ɗan adawa Garri Kasparow kuma yanzu haka a yanke masa hukuncin ɗaurin kwanaki biyar a kurkuku. Shi dai Kasparow daya daga cikin ƙusoshin wani ƙawancen ´yan adawa a Rasha, ya yi ƙoƙarin kutsa kai cikin wani shingen ´yan sanda don miƙa takardar koke-kokensa ga hedkwatar hukumar zaɓe, inda yake kira da a nuna adalci a zaben na ranar 2 ga watan desamba mai zuwa. Baya ga Kasparow an kuma kame wasu masu sukar lamirin gwamnati. Shaidu sun kuma ce jami´an tsaro a wasu birane sun yi awon gaba da mutane da yawa waɗanda suka so shiga cikin zanga-zangar da ´yan adawa suka shirya.