1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fiye da mutane 600 ake sanya wa ido saboda Ebola a Mali

November 18, 2014

Wannan na zuwa ne bayan da wani malami dan kasar Guinea da jami'ar lafiya da ta kula da shi suka rasu sakamakon wannan cuta ta Ebola a birnin Bamako.

https://p.dw.com/p/1DozZ
Mali Ebola Kourémalé Gesundheitspersonal
Hoto: Jan-Philipp Scholz

Bayan tsoron barkewar annobar Ebola kasar Mali na sanya idanu kan kusan mutane 600 saboda tsoron bazuwar kwayoyin wannan cuta me saurin kisa.

Jami'ai a kasar ta Mali bayan wani zama a jiya Litinin suna duba yadda zasu kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakarsu bayan kara samun wasu mutane biyu da suka harbu da kwayoyin cutar.

Kasar ta Mali dai na kara tsaurara matakan ne saboda tsoron kada wannan annoba ta kara yawa a kasar bayan da wani malami dan kasar Guinea da jami'ar lafiya da ta kula da shi sun rasu sakamakon wannan cuta ta Ebola a birnin Bamako fadar gwamnatin kasar ta Mali

A can Amirka ma mahukuntan sun bayyana shirinsu na sake inganta matakan bincike kan matafiya da ke shiga kasar daga yammacin Afrika.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu