1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fushin NATO kan hadewar Kirimiya da Rasha

March 19, 2014

Sakatare janar na Kungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya yi kakkausar suka game da yarjejniyar da ke mayar da Kirimiya karkashin ikon kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/1BSOt
Anders Fogh Rasmussen
Hoto: Reuters

Sakatare janar na Kungiyar Tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya soki matakin da Rasha ta dauka na sa hannu a kan yarjejniyar da ke mayar da tsibirin Kirimiya karkashin ikonta. A lokacin da ya ke bayani a cibiyar Kungiyar da ke da mazauninta a birnin Bruxelles, Rasmussen ya ce wannan mataki da ya danganta da gaban-kanta da Rasha ta yi, ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Hakazalika sakataren na NATO ya nuna bacin ransa dangane da mutuwar sojan Ukraine daya a lokacin wata musayar wuta da sojojin Rasha a wani sansanin sojoji da ke Simferopol babban birnin yankin Kirimiya.

Tuni dai shugaban kotun tsarin mulkin Rasha Valery Sorkin ya yi na'am da yarjejeniyar da aka sa hannu a kanta, wace ta mayar da Kirimiya a matsayin wani bangare na Rasha, ya na mai dangantashi da cewa ya dace da kundin tsarin mulkin kasa.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar Gamayyar Turai ke shirin yi karin haske a wannan larabar kan tallafin kudi da ta ke niyan bai wa Ukraine. Wannan kasa dai za ta fara samu kason farko na miliyan dubu da 600 na Euro daga EU domin ta samu ta tayar da komadar tattalin arzikinta da ke ckin wani mawuyacin hali.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar