1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Ali Bango na Gabon ya koma gida

Gazali Abdou Tasawa
January 15, 2019

Shugaba Ali Bango Ondimba na Gabon ya koma gida a wannan Talata bayan da ya kwashe watanni biyu da rabi yana jinya a kasar Maroko a sakamakon bugon zuciya da ya haddasa shanyewar wani sashe na jikinsa.

https://p.dw.com/p/3Bacm
Gabuns Präsident Ali Bongo
Hoto: Reuters/T. Negeri

 Wannan shi ne karo na farko da shugaban Ali Bango ya fito a bainal jama'a a aksar tun bayan da aka kwantar da shi a sakamakon bugon zuciya da ya yi sanadiyyar shanyewar wani sashe na jikinsa. Wannan dawowa ta Shugaba Ali Bango na zuwa ne kwanaki takwas bayan da wasu sojoji suka yi yinkurin kifar da gwamnatinsa. 

Sai dai ya zuwa yanzu ba san ko shugaban ya dawo daga jinyar ne baki daya ba ko kuma zai sake komawa jinyar a kasar ta Maroko. Tuni ma dai a wannan Talata Shugaba Ali Bango ya jagoranci bikin rantsar da ministocin gwamnatinsa 38 a fadarsa da ke a gabar teku. 

Sai dai kuma kafafan yada labarai na radiyo da talabijin na gwamnatin kasar ba su nuna bikin ba kai tsaye kamar yadda aka saba ga al'ada sannan ba a bai wa sauran 'yan jarida masu zaman kansu ba izinin halartar bikin ba a wannan rana. Bayan rantsar da ministoci Shugaba Ali Bango zai jagoranci taron majalissar ministoci na farko a cikin watanni uku da suka gabata.