1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gajiyar dake tattare da atisayen haɗin gwiwa na "Flintlock" a Nijar

March 10, 2014

A shekara ta 2015 Turai da Amirka suka hada kansu a yankin sahel domin karfafa matakan tsaro da zummar kawar da barazanar tsaron da yankin ke fiskanta

https://p.dw.com/p/1BMrZ
AFRICOM
Hoto: AP

A jamhuriyar Nijar, an kawo karshen atisayen sojojin duniya na
FLINTLOCK karo na 14, sojoji sama da dubu ne dai daga kasashen duniya 18 na Afrika da Amirka da kuma Turai suka halarci wanann atisaye na tsawon makonni ukku.

Tun a shekara ta 2005 ne dai manyan kasashen duniya a karkashin jagorancin kasar Amirka suka assasa wannnan shiri, a wani mataki na karfafa huldar sojojin kasashen duniya a cikin yaki da kungiyoyin yan ta'adda a kasashen nahiyar afrika musamman na yankin sahel.

Irin alkaryar da aka yi ta sha ke nan a gurin bikin kammala
wanann atisayen sojoji na flintlock wanda aka share
makonni ukku ana gudanar da shi a kasar ta Niger, atsiyan wanda ya wakana a cikin jahohin Tahoua mai iyaka da Kasar Mali da jahar Agadez mai iyaka da kasashen Libiya da Algeriya sai kuma jahar Diffa mai iyaka da jihohin Barno da Yobe masu fama da matsalar boko haram a makobciyar kasa Nigeria ya baiwa sojojin kasashen damar yin aiki kafada da kafada da kuma yin misayar ilimi dama samun horo a fannin sarrafa wasu makammai da misayar bayannai da dai sauransu.

Shugaban Ƙasar Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Ƙasar Nijar Mahamadou IssoufouHoto: Seyllou/AFP/Getty Images

Da yake jawabi a gurin bikin kammala wanann atsiye ministan tsaron kasar Niger Malam Mahamadu Karidjo ya ce kwalliya kam ta biya kudin sabulu.

Rawar rundunar tsaron Amirka ta Africom

Zentralafrikanische Republik Französische Truppen
Hoto: Getty Images/AFP/Miguel Medina

Rundunar tsaron kasar Amirka a sahel ta Africom ce dai ke jagorancin wanann shiri na flintlock, kuma da ya ke jawabi a gurin bikin rufe taron atisayen, Janar Hammer mataimakin kwamandan rundunar tsaron. Amirka a Afrika ya bayyan gamsuwarsa da shirin yana mai cewa:

"Tun a shekara ta 2015 kasashen Turai da Amirka sun hada kansu a
cikin yankin sahel domin yin aiki tare, domin karfafa matakan tsaro
da zummar kawar da barazanar tsaron da yankin yake fiskanta da abun da kuma zai kyautata halin rayuwar al'ummomin mazauna yankin ta yanda za su yi rayuwa ba a cikin tashin hankali ba, wannan ce ta sanya a wanann karo ko baya ga aikin soji muka nemi kusantar alummomin domin samun goyon bayansu a cikin wanann kokowa da ayyukan taaddanci a cikin yankin sahara kuma mun yi imanin hadin kan da su ka bamu zai yi matukar tasiri a cikin kokowar da kungiyoyin yan ta'adda".


Shi ma dai daga na shi bangare Shugaban hafsan sojojin kasar Nijar Janar, Seini Garba ya bayyan gamsuwarsa da rawar da shirin na flintlock ya taka wajen horas da sojojin kasar ta Niger musamman kokarin da sojojin shirin flintlock din su ka yi wajen ceto mutanen da hatsarin tashin nakiya da ya wakana a garin Iferouane lokacin sallar al'adu ta Air ya rutsa da su.

A takaice dai atisayen ya wakana ba tare da wata matsala
ba inda har ya kawo karshe ba tare da afkuwar wani hadari ba.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh