1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Turkiya da EU kan 'yan gudun hijira

Usman Shehu UsmanMarch 17, 2016

Ana shirin bude taro tsakanin kasashen Tarayyar Turai kan shawo matsalar kwararar baki, ta yadda za'a rika killace su cikin kasar Turkiya

https://p.dw.com/p/1IEQ2
Brüssel EU-Gipfel Ahmet Davutoglu Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Monasse

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya ce yana da yakinin kungiyar za ta cimma yarjejeniya da Turkiya don takaita kwararowar da baki yan gudun hijira ke yi cikin nahiyar Turai. Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bada cikakken goyon baya kan wannan shirin, inda ta ce, wata dama ce ta musamman ta magance matsalar korarar bakin. "Bisa tsari zai zama tilas ga Turkiya da ta dauke dukkan bakin da suka tsallako a tekun kasar Girka, Firimiyan Turkiya ya bada shawar cewa, ga dukkan dan Siriya da ya yi hijira a mai da shi cikin Turkiya. Wasu 'yan gudun hijiran ana iya mayar da su kasashen Turai bisa doka" To sai dai Merkel tana fiskantar suka daga cikin kasar ta Jamus dama a kungiyar EU kan wannan shirin, inda 'yan adawa ke cewa Turai na son tura 'yan gudun hijiran Siriya, cikin Turkiya wanda dama can ke da hanu dumudumu wajen ruruta rikicin Siriya, yayin da shugaban kasar Jamhuriyar Cek ke cewa ai in an yi haka to tamkar walakanta Turai ne aka yi.