1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin adawa da tura Sojoji Mali

October 19, 2012

Wakilan ƙasa da ƙasa na taro a Bamako, domin zartar da matakin amfani da ƙarfin soji a yankin arewacin Mali, dake ƙarƙashin 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/16TOm
Several thousand people march on October 11, 2012 in Mali's capital Bamako to call for armed intervention by a west African force to help wrest back the vast north from armed Islamist groups.The demonstrators carried banners and placards expressing support for the Malian army, Prime Minister Cheick Modibo Diarra and the Economic Community of West African States (ECOWAS), which is preparing to send troops if it gets the backing of the United Nations and western countries. AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE (Photo credit should read HABIBOU KOUYATE/AFP/GettyImages)
Hoto: Getty Images/AFP

A wannan juma'ar ce ake gudanar da wani muhimmin taro na ƙasa da ƙasa a birnin Bamako na ƙasar Mali, domin zartar da yiwuwar amfani da karfin soji a yankin arewacin kasar, dake karkashin ikon masu fafutukar neman 'yanci. Mahalarta taron yini gudan, sun haɗar da shugaban gwamnatin rikon kwarya na Mali Dioncounda Traore, da wakilan ƙungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, MDD da tarayyar Turai. A cewar shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma, tattaunawar na da nufin taimaka wa Mali sake kasancewa kasa ɗaya, ta hanyar wanzuwar zaman lafiya. Ya kara da cewar, idan ba an gano bakin zaren warware rikicin na Mali da wuri ba, ƙasashen yankin dama nahiyar na fuskantar barazanar yaɗuwarsa. Tun a ranar alhamis ne dai dubban al'ummar kasar suke gudanar da gangamin nuna adawa da tura dakarun ketare zuwa birnin Bamako. A makon daya gabata ne dai, komitin sulhu na Majalisar Ɗunkin Duniya, ya bawa hukumomin Mali wa'adin kwanaki 45, na tsara yadda sojojin ketare zasu shiga ƙasar. A yanzu haka dai, Sojojin ƙungiyar ECOWAs 3,300 ne suke cikin shirin kota kwana, na afkawa cikin ƙasar ta Mali bisa ga umurni.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita : Umaru Aliyu