1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargadi kan aikin hajji bana

Usman ShehuJune 17, 2014

Masana harkar kiwon lafiya na kara bayyana damuwar kan cutar da ke yaduwa a Saudiyya da yadda hakan zai iya shafara mahajjata

https://p.dw.com/p/1CK03
MERS Virus
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kungiyar kula da lafiya ta duniya, wato WHO, ta nuna damuwar kan cutar mura da ake kara samun ta a kasar Saudiyya, inda kungiyar ta lafiya ta ce hakan wani abun damuwa ne musamman ga wadanda ke shirin zuwa hajjin bana. A cewar hukumomi, kawo yanzu mutane 800 suka kamu da wannan cutar, kana daga cikinsu kimanin 300 sun mutu. Akasarin wadanda cutar ta shafa, suna kasa mai tsarki ne. Cutar wanda aka sani da MERS a takaice, ta na jawo katsewar numfashi, kuma ta na sa mura da zazzabi da nimoniya. A yanzu haka bayan kasar Saudiyya inda cutar ta fara barekewa, ta kuma bazu zuwa kasashe makobta da Turai da Amirka.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu