1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargadi kan sabon juyin mulki a Burundi

Ahmed SalisuJune 1, 2015

Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi ya yi zargin cewar wasu na yin wani sabon yunkuri na ganin sun kifar da gwamnatin ta hanyar yi mata juyin mulki.

https://p.dw.com/p/1FaON
Burundi Präsident Pierre Nkurunziza
Hoto: Getty Images/AFP/F.Guillot

A wata sanarwa da ya fidda dazu, shugaban na Burundi ya ce dukannin wani shiri na kifar da gwamnatinsa ba zai yi tasiri ba, inda ya bukaci 'yan jam'iyyarsa da su sanya idanu don ganin mulki na dimokradiyya a kasar ya cigaba da wanzuwa.

To sai dai duk da wannan kashedi nasa da ma bukatar da ya ce ake da ita ta kare tsarin dimokradiyya a kasar, 'yan dawa da kungiyoyi na fararen hula na cigaba da sukarsa kan abinda suka kira yin karen tsaye ga kundin tsarin mulki ta hanyar neman wani sabon wa'adin mulki da suka ce ya saba ka'ida.