1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar cin kofin ƙwallon ƙafa a Afrika

January 21, 2013

Masar ta fi ko wace ƙasar Afirka yawan ɗaukar kofi a gasar cin kofin ƙwallon ta Afirka

https://p.dw.com/p/17NyQ
Afrika Cup 2013 (Logo)

Daga cikin ƙasashen da ke halartar gasar cin kofin ƙwallon ƙafar Afrika a ƙasar Afrika ta Kudu, wace ƙasa ta fi ɗaukar wannan kofi.

A shekara 1957 ne a ƙasar Sudan a ka shirya karon farko na gasar cin kofin ƙwallo ta Afrika, kuma ƙasar Masar ce ta fara lashe kofin bayan ta lashe Ethiopiya a karon ƙarshe.

Tun daga nan Masar ta fara yiwa sauran ƙasashen Afirka fintinkau ta fannin ƙwallo.Da farko zuwa yanzu wannan itace gasa ta 29.Masar ita ce ta fi yawan ɗaukar kofi, domin ta ɗauka har sau bakwai, ta biyu itace Ghana wadda ta ɗauka so huɗu, itama Kamaru ta ɗauka so huɗu, sannan sai Najeriya da Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo ko wace ta ɗauka so biyu, akwai ƙasashe Tara wanda su ka taɓa ɗaukar wannan kofi so guda, wannan ƙasashe kuwa sune Cote d´Ivoire,Zambiya wadda ke riƙe da kofin a yanzu, akwai Sudan, da Tunisiya, sannan sai Aljeriya da Ethiopiya da Maroko da Afirka ta Kudu da Kongo Brazaville.

A wannan karo na 29 ba a san mai ci tuwo ba sai miya ta ƙare.

Sannan akwai ƙasashe Biyar wanda su ka taɓa kaiwa ga karon ƙarshe amma ba su yi nasara ɗaukar kofi ba, wannan ƙasashe biyar sune Mali , Yuganda,Guine, Libiya da Senegal.

Mawallafi: Yahouza sadissou Madobi
Edita: Usman ShehuSUsman