1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar cin kofin 'yan kasa da shekaru 20

July 24, 2013

An fara wannan gasa ta cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru ashirin ne a shekara ta 1977 kuma hukumar kwallon kafa ta duniya ta FIFA ce ke shiryata.

https://p.dw.com/p/19DgX
France's team players celebrate with trophy their victory over Uruguay in the final match of the FIFA Under-20 tournament in Istanbul, July 13, 2013. REUTERS/Osman Orsal (TURKEY - Tags: SPORT SOCCER)
Finale der U 20-WM zwischen Frankreich und UruguayHoto: Reuters

Ita dai gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan shekaru kasa da 20 wadda FIFA ke shirya an soma ta ne a shekara ta 1977 domin bawa matasa na kasashen duniya daban-daban da ke taka leda damar gudanar da gasa tsakankaninsu don fidda gwani.

Kasar Tunisia da ke arewacin Afrika ce ta fara daukar nauyin gasar a shekarar ta 1977 inda kasashe goma sha shidda su ka kece raini a gasar. Uku daga cikin kasashen kuwa sun fito ne daga nahiyar Afrika wanda suka hada da Tunisiya mai masauki baki da Cote D'Ivoire da kuma kasar Morocco.

Samstag 09.07.2011, FIFA Frauen-WM, Viertelfinale der Frauen Fussball - Weltmeisterschaft 2011 in Wolfsburg, Deutschland - Japan 0:1 n.V., Deuschland Fans Foto: DeFodi.de
Magoya bayan 'yan wasan JamusHoto: picture-alliance/DeFodi

Wasan farko da aka buga a gasa ta farko ta cin kofin na 'yan kasa da shekaru ashirin dai an yi shi ne tsakanin kasashen Faransa da Spain wanda aka yi ranar 27 da gawatan Yuni na ita wannan shekara ta 1977 an kuma tashi daga wasan Spain na da ci biyu yayin da Faransa ke da ci daya.

Wasan karshe kuwa na wannan gasa an yi shi ne tsakanin kasar Mexico da Tarayyar Soviet ta wancan lokacin kuma Tarayyar ta Soviet ce ta kai ga lashe gasar musamman da taimakon dan wasan tsakiyar nan nata Vladmir Bessonov wanda aka yi ittifakin cewar tauraruwarsa ta fi ta kowa haskakawa a gasar.

Kasar Mexico ita ce ta zo ta biyu a gasar sai kuma Brazil da ke goya mata baya a gasar. Ita dai wannan gasa ta cin kofin duniya na FIFA na matasa 'yan kasa da shekaru ashirin ana yinta ne bayan kowacce shekara biyu sabanin shekaru hudu da ake yin asalin gasar cin kofin duniya ta manya da aka saba gani.

Daga jerin kasashen da su ka dauki nauyin gasar akwai Japan wadda ta dauka a shekara ta 1979, Australia 1981 da Mexico 1983, Tarayyar Soviet 1985 sai Chile a shekara ta 1987 da Saudi Arabiya wadda ta karbi bakuncin gasar a shekara ta 1989.

Malian players celebrate with their bronze medal at the end of the 2013 African Cup of Nations third place final football match Mali vs Ghana, on February 9, 2013 in Port Elizabeth. Mali won 3 to 1. AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO (Photo credit should read ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images)
'Yan Afrika sun taka rawa a gasarHoto: Getty Images

Sauran kasashe sun hada da Portugal a 1991 da Australia a karo na biyu a shekara ta 1993 Daular Qatar 1995, Malaysia a shekara ta 1997 sai a shekara ta 1999 ne tarayyar Najeriya ta kasance kasa ta biyu a kasashen Africa da su ka dau bakucin gasar.

Baya ga wadannan kasashe, sauran kasashen duniya daban daban sun yi ta daukar nauyin shirya gasar har kawo wannan shekara ta 2013 da mu ke ciki wadda kasar Turkiyya ta dauki nauyi kuma aka kammala a 'yan kwanakin da su ka gabata wanda inda kasar Faransa ta samu nasarar daukar kofin karonta na farko yayin da kasar Uruguay ke take mata mata baya sai kuma kasar Ghana da ta zo ta uku.

Daga cikin kasashen da su ka fi daukar kofi a wannan gasar akwai Argentina wadda ta daga kofin har sau shidda sai kuma Brazil da ta samu nasarar lashe gasar sau hudu.

Argentina's Lionel Messi goes for the ball during a group A Copa America soccer match against Costa Rica in Cordoba, Argentina, Monday, July 11, 2011. Argentina won 3-0. (Foto:Natacha Pisarenko/AP/dapd)
Argentina ce ta fi kowa daukar kofiHoto: dapd

Kasar Ghana ita ce kasar Afrika daya tilo da ta kai ga lashe wannan gasa inda ta samu wannan nasara a shekara ta 2009 lokacin da kasar Masar ta dauki bakuncin gasar sai dai wasu kasashen Afrika irinsu Tarayyar Najeriya da Masar da Mali sun taka rawa ta a zo a gani a lokuta daban-daban daga lokacin da aka somo gasar kawo wannan lokacin.

Mawallafi: Ahmed Salisu

Edita: Zainab Mohammed Abubakar